✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarrafa Albarkatun Gona: karo

karo wani abu ne mai danko da ake samu daga jikin wadansu itatuwa, musamman ma bagaruwa, a arewacin Najeriya, da makwabtan kasashe. Najeriya ce ta…

karo wani abu ne mai danko da ake samu daga jikin wadansu itatuwa, musamman ma bagaruwa, a arewacin Najeriya, da makwabtan kasashe. Najeriya ce ta biyu a duniya wajen samar da karo da kuma sayar da shi a kasuwannin duniya, bayan kasar Sudan, inda ta e samar da tan dubu 200 daga cikin tan dubu 700 da ake samu a duniya. Ana samun karo a jihohin Yobi da Barno da Bauchi da Jigawa da Adamawa da Gombe da Zamfara da Neja da Nasarawa da Katsina da Kebbi da Taraba da Sakkwato da Filato.
karo na da takaitaccen amfani a gargajiyance, babbar kafar amfani da shi ita ce yin tawadar rubutun Arabiyya. Amma karo na da matukar mahimmanci a masana’ antu na cikin gida da na kasashen ketare, saboda haka ya na da babbar kasuwa. Masana’ antu na sarrafa karo wajen yin magunguna da kayan shafe-shafe da kayayyakin abinci da kayayyakin sha. Sauran hanyoyin da masana’antu ke amfani da karon da suka sarrafa sun hada da abubuwan da ke sa kaurin sinadarai da yaukaka su da inganta su. Masana’ antun kuma na amfani da karo wajen yin abubuwan sa kamshi a cikin abubuwan ci da na sha, da kuma yin kayayyakin lashe-lashe irin su alawa da makamantansu.  
Wannan amfani da karo yake da shi ya sa masana’ antu ke nemansa ruwa – a- jallo, musamman ma a kasashen Jamus da Japan da Indiya da Faransa da Ingila da Sifen da Bangaladesh da Pakistan da Italiya da kasar Sin (China). Ana sayen karon Najeriya a kasashen Beljiyom da Sin da Amurka da Ingila da Japan.
Ana samun launin karo masu daraja kashi uku a Najeriya, kamar haka: Giredi Wan (Grade 1, da Turanci ko Acacia Senegal) Giredi tu (Grade 2, da Turanci, ko Acacia Seyal) da kuma Giredi siri (Grade 3, da Turanci, ko Combretum). Zan yi karin bayani game da ire-iren launin wadannan karon.   
Saboda muhimmancin da Najeriya ke da shi a kasuwar karo ta duniya, Gwamnatin Tarayya ta fito da tsarin noma da kasuwancin karo domin inganta hanyoyinta na samun kudin shiga da ba ta hanyar fitar da gurbataccen mai ba, da ake cewa ‘Nigeria Gum Arabic Sector Debelopment Program’. Makasudin wannan tsarin shi ne a taimaki manoman karo da masu sarrafa karo da masu fitar da karo zuwa kasashen waje, su inganta yawa da martabar karo giredi wan domin sayar da shi a kasuwannin Amurka. Akwai kamfanin ‘ARD Inc’ na Amurka da ke aiki da manoma da masu fitar da karo kasashen waje a duk sassan kasar nan da ake samun karo, domin samun biyan wannan bukatar.    
kudurin wannan tsari shi ne:
1.      Tabbacin ingancin karon da Najeriya za ta sayar wa masana’antun Amurka;
2.      A karfafa gwiwar masu harkar karo wajen samar da shi da inganta shi da bunkasa kasuwarsa. Wannan zai samar da kudin shiga ga kasar daga kasashen waje, ya samar da arziki ga masu harkar karo da samar da aikin yi;
3.      Taimakawa wajen dasawa da kula da bagaruwar samun karo a wuraren da Hamada ke kwararowa domin dakatar da ita a samu sukunin yin noma.
Zan tsaya a nan sai Allah Ya kai mu makon gobe.