✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarrafa Albarkatun Gona: Kiyaye Ka’idoji (2)

A kasidar makon jia na fara duba ka’idojin da dan kasuwa zai kiyaye da su wajen sarrafa albarkatun gona domin sayarwa a kasuwannin gida da…

A kasidar makon jia na fara duba ka’idojin da dan kasuwa zai kiyaye da su wajen sarrafa albarkatun gona domin sayarwa a kasuwannin gida da na kasashen ketare. Kamar yadda na yi shimfida a kasidar, zan fadakar da dan kasuwa game da irin ka’idojin da suka kamata ya kiyaye yayin tafiyar da wannan harka, sannan kuma in rika daukar irin wadannan albarkatun gona da dai-dai da dai-dai ina bayanin yadda za a iya samunsu da inda za a iya samunsu da kuma kasuwannin da ake bukatarsu.
    Na ja hankalin dan kasuwa a kasidar cewa, masu bukatar wadannan kayayyaki mutane ne masu ka’ida, saboda haka bin ka’idar da su ka ajiye akan wannan hajja zai kasance alheri ga dan kasuwar da ke yin wannan harka. Na yi bayani a kan ka’idojin fitar da irin wadannan kayayyaki zuwa kasashen ketare, da kuma bayani a kan matsalar da ke biyo bayan rashin  bin ka’idar a cikin harkar. Yau kuma zan yi bayani a kan cika ka’idar ga masu sayen irin wadannan kaya a kasuwanninmu na cikin gida.     
    A kan samu kayayyakin gona da aka sarrafa a manyan kantuna (Supermarkets) wani lokacin ma a manyan kantunan magani (chemists) ko kuma a kasuwannin Turawa da ke manyan garuruwa da biranen kasar nan. Wadannan wurare da na lissafa, wurare ne da masu hannu-da-shuni da ‘yan boko da matansu da ‘ya‘yansu da baki ‘yan kasashen waje ke sayayya. Akwai wani abu tattare da irin wadannan mutanen: suna da kudi kuma a shirye suke da su sayi duk abin da ransu ya yi musu dadi a kai. Albarkatun gona da aka sarrafa ake sayarwa a wadannan kasuwanni sun hada da kayan miya da na marmari da citta da tafarnuwa da zuma da nonon shanu da naman shanu da na tumaki da awaki har ma da na kaji da talotalo.
    Babbar ka’idar shiga wannan kasuwa ita ce tsabtace kayan da dan kasuwa zai sayar a irin wadannan kasuwanni, wannan shi ya bambanta su da sauran kasuwanni. Tsabta a nan ta hada da tsince dukkanin wani haki ko wani datti ko kasa da kura da ka iya tahowa a cikin kayan. Misali, za ka ga doya da tabon gonar da aka tono ta ya mamaye ta, an kasa a kasuwa ana jiran mai saye. Za kuma a iya ganin wake ko gyada tare da wadanda kwari suka ci, ba a tsince ba; ko kuma tumatiri ciki da rubabbu ko wadanda suka fashe, ba a tsince ba, ko ma ba a wanke ba. Amma ba za ka ga irin haka ba a irin kasuwannin da na yi maganarsu a baya ba. dan kasuwa ya kuma fahimce cewa sarrafa albarkatun gona, kamar yadda za a gani a gaba, ya hada da tsaftace su ta hanyar tsince tarkacen da ke cikinsu da wanke su. Za kuma a gani nan gaba cewa sarrafa wadansu daga cikin arbarkatun gonar da ma za a fitar da su kasashen ketare bai fi tsincewa da wankewa ba.
    To lalle irin masu sayen kaya a kasuwannin zamani da na lissafa ba za su sayi kayan da ba a gyara ba, shi ya sa suke tafiya irin wadannan kasuwanni domin sayen tsabtatattun kaya. Abin lura ga dan kasuwa a nan shi ne, wadannan abokan ciniki a shirye suke da su biya farashi fiye da wanda za su biya a sauran kasuwanni. Kuma ba su da wahalar hulda kamar sauran masu sayan kaya a sauran kasuwanni, inda za su yi ta tayawa suna neman sauki. Irin wadannan kasuwanni na da tsayyen farashi wanda mai saye ba ya tayi. A takaice dai wannan na nuna wa dan kasuwa kasancewar riba mai tsoka a cikin harkar.
    Wata ka’ida kuma ta wannan kasuwa ita ce, ta zabo kayayyaki masu girma kuma masu kyau da za su jan hankalin mai saye. Sai kuma amfani da mizani, wato ma’auni, musamman ma kamar kayayyakin da za su aunu, kamar nama da kayan marmari da za a iya sayarwa da sikeli a kan awon kilo-kilo. Sai kuma irin su zuma da man ja da na kuli-kuli da za a iya aunawa lita-lita.