✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarrafa Albarkatun Gona: Tafarnuwa (3)

A makon da ya gabata na yi bayani a kan iri-iren tafarnuwa da ake samu a kasashen duniya, musamman ma a gida Najeriya, tare da…

A makon da ya gabata na yi bayani a kan iri-iren tafarnuwa da ake samu a kasashen duniya, musamman ma a gida Najeriya, tare da darajarsu, na kuma  yi wa dan kusuwa mai niyyar shiga harkar saye da sayar da tafarnuwa bayanin yadda zai sarrafa ta domin samun alherin da ke cikin harkar. A wannan makon kuwa zan tashi ne  a kan duba farashi da kasuwar tafarnuwa a ciki da wajen kasar nan.
Farashin tafarnuwa na kamawa daga Naira dubu 180 a kakarta ya zuwa Naira dubu 250 a tan, idan ta taho karewa, kuma wannan farashi ya danganta da wurin da  dan kasuwa ya sayi tafarnuwarsa da kuma lokacin da ya sayi tafarnuwarsa. Ga dan kasuwar da zai fara wannan harkar, kada ya yi tsammanin samun tafarnuwa a kasuwanninmu da ake noma ta an ajiye masa tan-tan ya saya, inda zai misalta da farashin tan da aka ba shi a wannan shafin.  A’a, dan kasuwa zai samu tafarnuwa a cikin mazubai iri-iri, illa kawai ya yi amfani da basirar shi ya cim ma farashi madaidaici.
   A irin wadannan kasuwanni da garuruwa da ake samun tafarnuwa, misali, garin  Kofa da ke karamar hukumar Bebeji ta Jihar Kano, dan kasuwa zai samu tafarnuwa a cikin kwanuka da kwanduna yara na talla. Akwai kuma wacce za a iya samu a hannun manya da kananan ‘yan kasuwa a cikin buhuna manya da kananana a kan farashi daban-daban. Abin lura ga dan kasuwa a nan shi ne, ya zama dole dan kasuwa ya nazarci kasuwar da zai ciniki a cikinta na dan karamin lokaci kafin ya fara sayen kaya. dan kasuwa zai lura da farko cewa wace irin tafarnuwa ce a kasuwar? Zai lura ko ta yi daidai da launin da abokan cinikinsa suka ba shi oda. Yaya farashin da ke tafiya a kasuwar  a wannan lokaci, domin kada ya sayi kaya a farashin da ya wuce na kasuwar a wannan ranar a kuma wannan lokacin. Ya kuma zama dole dan kasuwa ya lura da tsabtar tafarnuwar da zai saya, ya kuma tabbatar da kowane farashi ya yi daidai da tsabtar tafarnuwar da zai saya. Misali, ba zai sayi tafarnuwa mara gyara a farashi daya da gyararriya, wacce babu wata wahalar da zai yi mata ba.      
    Farashin tan din tafarnuwa a kasuwannin duniya na kamawa daga dalar Amurka  2,200 ya zuwa dala 2,500 har fiye, ya danganta da irin tafarnuwar da kyan tafarnuwar da kuma lokacin da ake bukatarta . Zan shawrci dan kasuwa a nan da ya kasance ya san farashin tafarnuwa a kasuwannin kasashen waje a lokacin da ya samu oda, musamman ma farashin kasuwannin Amurka tun da ita ce kasuwar tafarnuwa mafi girma, wacce kuma ‘yan kasuwar Najeriya suka fi hulda a ciki. dan kasuwa zai samu wannan farashi a dandalin tafarnuwa na yanar gizo.
    Akwai kuma kungiyar hadin gwiwa tsakanin gwamnatocin Amurka da Kanada da wadansu kasashen a gefe daya da kuma ‘yan kusuwar kasashen da kuma kungiyoyi masu zaman kansu da ke sha’awar huldar tafarnuwa, da ake ce wa, ‘Edport Path’.   An kafa wannan kungiya ta hadin gwiwa domin samar wa ‘yan kasuwa masu bukatar kayayyaki irin haka daga kasashen Amurka da Kanada, da kuma inganta kasuwancin kayayyaki irin haka a tsakanin wadannan kasashe da kasashe masu tasowa da ke samar da su.
    dan kasuwa zai iya lalubar wannan kungiya a yanar gizo domin tambayoyi da karin bayani a kan harkar tafarnuwa, walau anan gida Najeriya ko a kasuwannin kasashen waje.