✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sarrafa Albarkatun Gona

A wannan makon zan fara makala a kan yadda dan kasuwa zai iya sarrafa albarkatun gona domin sayarwa a garin da yake, ko a manyan…

A wannan makon zan fara makala a kan yadda dan kasuwa zai iya sarrafa albarkatun gona domin sayarwa a garin da yake, ko a manyan biranen kasar nan, ko ya fidda su zuwa kasashe makwabtanmu ko kasashen ketare. Idan mai karatu bai shafa’a ba, na yi wadansu makalu kimanin shekaru biyu da suka gabata a kan yadda dan kasuwa zai iya sarrafa wadansu albarkatun kasar nan domin fitarwa zuwa kasashen waje. Kuma a baya-bayan nan na yi mukalu da ke bayani a kan irin tallafin da dan kasuwa zai iya samu daga wadansu hukumomin gwamnati da kungiyoyi wajen fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, musamman ma kasashen Yammacin Afirka domin inganta cinikayyar sashe-sashe na duniya.
    Bahaushe kan ce magani a gonar yaro sai ya fito yaro bai sani ba ya nome. Za ka rika jin ‘yan kasuwa na kukan babu kasuwa, ko matasa na cijigiyar abin da za su yi domin dogara da kai, walau sana’a ko aiki, ko kuma masu jari na cigiyar inda za su zuba shi domin samun riba. Irin wadannan koke-koke da cigiyoyi na faruwa ne saboda rashin sanin alherin da Allah Ya yalwace mu da su a cikin wannan kasa tamu Najeriya. Kuma wani abun mamaki budadde da kowa ya sani shi ne yadda ba mu iya sarrafa wadannan albarkatu da Allah Ya arzurta mu da su a cikin kasar nan. Kuma wani abun godiya Sarki Allah shi ne, ba wai a wata shiyya ko a wani wuri ko wadansu wurare kalilan Allah Ya zuba wadannan albarkatu ba, a’a suna nan a kowace jiha, a kowace karamar hukuma, a kuma kowane lungu da sako na kasar nan.
    To bari mu zagaya Najeriya mu ga irin wadannan albarkatu da Allah Ya wadata mu da su, na gona kawai, ba ma na ma’danai ba. Idan mai karatu a yankin Arewa maso Yammacin Najeriya yake, akwai albasa da ridi da auduga da gyada da mangwaro da tumatur da dabbobi kanana, kamar awaki da tumaki, da kuma manyan dabbobi irinsu shanu da rakuma. Kafin mu bar wannan shiyyar, wanda ke zaune cikinta ko wanda ya santa zai ce mangwaro da albasa da tumatir na lalacewa a wannan yakin kowace shekara saboda rashin yadda za a yi da su idan kakarsu ta yi, musamman ma a jihohin Kebbi da Kano da Jigawa. Abin da asar Burkina Faso ta ke samu daga mangwaron da take fitarwa kasashen ketare, wanda kuma bai kai kyan na Najeriya ba, ko ya kai yawan na jihohin Kano da Jigawa ba, ya fi kason kudin da jihohin Arewa 19 suke samu a shekara daga kudin man fatur.
    A shiyyar Arewa maso Gabas kuwa, akwai karo da waken suya da kifi da nonon shanu da tattasai (dan Damaso) da shanu da wake da shayi da gahawa da furen kallo (flower da Turanci). A wadansu sassa na Jihar Adamawa da ke wannan shiyyar ana tatsar madarar shanu a zubar domin shanun su samu lafiya, domin kuma babu masu saye a kusa, babu kuma yadda za a sarrafa ta a ajiye, ko a kai ta kasuwannin nesa inda ake bukatarta. Najeriya na kashe miliyoyin Daloli (biliyoyin Nairori) domin shigowa da madara daga kasashen duniya, musamman ma kasar Denmark. Su kuwa kasashen Norwegian da suka hada da Denmark da Holland da Norway, na samun kudin shiga daga madarar shanu da dangoginta fiye da yadda Najeriya ke samu daga danyan man fetur. Sannan kuma kasar Kenya da ke nan Afrirka na samun kudi daga fitar da furen kallo a shekara, fiye da yadda jihohin wannan shiyya ke samu daga kason man fetur daga alaben Najeriya.
   Wani abin lura ga mai karatu shi ne, duk wadannan albarkatu na gona da wadannan kasashe ke sayarwa a kasuwannin duniya ba wai gwamnatin kasashen ke sarrafa su ba su kai kasuwannin duniya. A’a ‘yan kasuwar kasar ne manya da matsakaita da kanana ke sarrafa su, su sayar wa da duniya. Zan ci gaba da zagaya sauran sassan kasar hudu da suka rage a makon gobe, kamar yadda na zagaya biyu daga cikinsu a wannan makon, inda zan duba albarkatun gonarsu, sannan kuma in ba dan kasuwa, musamman ma karami da matsakaicin dan kasuwa yadda zai iya sarrafa wadannan kayayyaki domin kasuwanninmu na gida da na kasashen waje.