Da Dumi Dumi

Sarrafa tumatur na fuskantar barazana a Najeriya – Sabon Bincike

Tumatirin da yake lafiya kalau
Tumatirin da yake lafiya kalau

Wani sabon bincike da rukunin wadansu masana kimiyya daga kasar Kenya da Najeriya suka gudanar da aka wallafa a makonnin baya a wata mujalla ta Intanet ya nuna cewa an samu bullar wata cutar da ke kama tumatur mai suna Tuta Absoluta, inda suka ce babbar cuta ce da ta dabaibaye tumatir a kasar nan.

Rahoton mai taken “Tuta Absoluta Lepidoptera Gelachiidae” an gabatar da shi ne a wata babbar cibiya ta binciken kwari ta duniya da ke Nairobi a kasar Kenya.

Cibiyar Kimiyyar Sanin Harkokin Tsirrai da Bincike da ke Ibadan a Najeriya, ta yi gwaje-gwajen wasu gonaki a tsakanin watannin Maris din shekarar 2017 zuwa Yulin 2018 domin raba irin tumatir da Tuta Absoluta.

Wadansu masana kimiyya, Pascal Osa da Aigbedion Atalor da Abiola O., da Oladigbolu Adejumo da A. Layede da Igho B. Igbinosa da Samira A. Muhammed ne suka wallafa wani bincikensu da suka yi a mujallar Cututtukan Tsirrai da Kariya (Plant Diseases and Protection).

Sun gano cewa a Kudancin Amurka, akwai wata cuta mai suna Pinworm da take kama tumatir sa’annan cutar Tuta Absoluta wadda wata mummunar cuta ce tana kama tumari a Najeriya.

ADVERTISEMENT

Wannan bincike an gudanar da shi ne a bangarori daban-daban har guda 528 a jihohi 11 na Najeriya; sa’nnan aka wallafa sakamakon a yanar gizo a ranar 17 ga watan Agustan wannan shekarar a wannan mujalla ta Plant Diseases and Protection.

Masanan sun kuma bayyana cewa sakamakon, ya nuna cewa an samu maganin feshin wannan cutar. Akwai shi kuma a sassa 360 na Arewa da Kudancin Najeriya.

Sun kuma bayyana cewa wannan cutar na yaduwa cikin sauri kamar yadda aka gano a lokacin bullarta a shekara ta 2015, sannan suka kara bayanin cewa saboda wannan cutar dake kama tumaturi ya sa baya jimawa yake lalacewa.

Share