✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sasha Pesic: Mai kula da karnuka sama da 750

Wani mutum mai suna Sasha Pesic, a kasar Serbia yana kula da karnuka sama da 750 a wani mataki na nuna  tausayawa ga  karnukan da…

Wani mutum mai suna Sasha Pesic, a kasar Serbia yana kula da karnuka sama da 750 a wani mataki na nuna  tausayawa ga  karnukan da aka yi watsi da su ba tare da kula ba.

Sasha ya fara kula da karnunkan new bayan da ya tsinci wani dan kuikuyo a  shekarar 2008, fiye da shekara 10 da suka gabata, inda zuwa bana ya ceto ’ya’yan karnuka sama da 1,200 kuma yanzu haka yana kula da karnuka 750 da ya tsinto.

Sunan Sasha Pesic ya fara shahara ne a duniya kan abin da yake yi a shekarar 2015, bayan ya sanya wani bidiyo yana ciyar da karnukan, inda bidiyon ya yi matukar tasiri musamman a kafafen sada zumunta na zamani. Akalla sama da mutum miliyan 63 ne suka kalli wannan bidiyo a shafin Facebook kadai. Ban da wajen kasar Serbia ko kuma birnin Nis da yake zaune, kowa ya san kowane ne Sasha a garin inda yake lura da sama da karnuka 100.

Sasha ya sadaukar da rayuwarsa wajen taimaka wa karnukan da ba su da gata ne, hakan ya sa ya raini karnuka sama da 1,200 inda mutane daga sassan duniya suka karbi karnuka 400 daga cikin wadanda ya kiwata, yanzu kuma yana ci gaba da kiwon sama da karnuka 750, lamarin da ya sa ya ce yana neman taimako don ci gaba da kula da karnukan.

Sasha, yana kashe  Dalar Amurka dubu 11 da 150 (kimanin Naira miliyan 4 da dubu 53 da 844)  duk wata wajen ciyar da karnukan ban da kudin magungunan da yake saya sannan yana biyan ma’aikatan da suke tsabtace muhallin da karnukan suke  zama.

Wani lokacin yana samun gudunmawa daga wajen  jama’ar kasashen waje. Sannan wadansu makwabtansa kan saki karnukan u kusa da inda yake kiwon nasa karnukan saboda sun san ba zai bar karnukan su tagayyara ba.

“Wadansu mutanen yankin suna sha’awar su kasance tare da karnukan da aka yi watsi da su, bayan sun fahimci yadda Sasha ya tanadar musu da muhalli.” Kamar yadda ya bayyana wa kafar sadarwa ta Niske Besti.

Wadannan karnukan idan dare ya yi suna kwanciya ne a wani sansanin da aka kebe musu. Sasha, ya ce “Karnuka halittu ne da suke bukatar kula don haka nake lura da su yadda ya dace.

Na dade ina neman tallafin jama’a, amma sai ya kasance jama’a na watsi da bukatata, sai daga bisani suka fara jin hidimar da nake yi wa tsintattun karnukan.”

Sai dai Sasha, ya yi sa’ar samun gudunmawa daga masu sha’awar kiwon dabbobi daga kasashen waje. Wadansu da dama daga kasashen duniya suna kokarin bayar da tallafin kudin duk wata. Sannan da karin samar da wuraren kula da karnukan. Ta hanyar kamfe Sasha, yana samun tallafin gidajen kula da karnukan, amma duk da haka bai cimma burinsa ba.

Sasha ya mika godiyarsa ga jama’ar da suke ba shi tallafin muhallin da yake kiwon karnukan, duk da haka wajen kiwon karnukan ya yi kadan saboda cinkushewar karnukan.

Sasha, ya ce duk ya san sunayen karnukansa kuma duk inda ya gansu zai gane su, kullum burinsa shi ne ya tabbatar da ya dauki nauyinsu.

Sasha, ya kara da cewa soyayyar da yake wa karnukan ya sa yake kula da lafiyarsu abincinsu da wajen kwanansu.