✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Satar baburan ’yan acaba na karuwa a Bauchi

Wadansu daga cikin masu sana’ar acaba sun koka kan yadda wadansu batagari ke karbe baburan a hannunsu wani lokacin ma har ya kai ga kisa…

Wadansu daga cikin masu sana’ar acaba sun koka kan yadda wadansu batagari ke karbe baburan a hannunsu wani lokacin ma har ya kai ga kisa ko rauni a Jihar Bauchi.

’Yan achabar sun bayyana haka ne lokacin da suke zantawa da Aminiya  a Bauchi, inda suka yi kira ga Gwamnatin Jihar ta yi duk abin da za ta iya domin ganin an shawo kan matsalar ta yadda za su samu sukunin gudanar da sana’arsu ba tare da fuskantar wata barazana ba.

Sani Mohammed Abdullahi, shi ne Sakataren Kungiyar ’Yan Acaba da Keke NAPEP da ke Kofar Cibil Defence a Bauchi, ya ce, “Gaskiya mu ’yan acaba muna fuskantar matsaloli masu yawa, wani lokaci a kan dauki mutum a ce masa wuri kaza, a shigar da shi lungu a samu wadansu sun tsaya a wajen yana isowa sai su buge shi su kwace babur din. Daga bara zuwa bana, mun rasa mutane da dama sakamakon buge su da aka yi aka kwace abin hawansu, wadansu kuma sun ji munanan raunuka. A kwanan baya ma an samu mutum bakwai da aka buge su ba a san ma daga inda suka fito ba saboda ba su da katin shaida, sai da magabatanmu suka je suka sa hannu a dakin ajiye gawarwaki sannan aka bada gawarwakinsu aka binne su.”

Ya ce, “A kwanan baya akwai wani makwabcina  ga gida ga gida da aka buge shi an kwace babur dinsa na halarci jana’izarsa, wani lokaci hoda suke fesa wa mutanenmu. Ko a watan jiya akwai wani a yankinmu an fesa masa ya fadi aka tafi da babur dinsa ya kai kusan mako biyu kafin ya farfado.”

Sakataren ya ce wasu daga cikjin barayin baburan na amfani da salo iri -iri suna kashe mambobinsu suna kwace musu babura.

Abdullahi ya ce jami’an tsaro suna daukar mataki da zarar sun kai musu rahoto, inda ya ce suna bakin kokarinsu kan wannan lamari.

A cewarsa, “Matakan da muka dauka don rage matsalar su ne kullum muna wayar da kan ’yan acaba cewa su daina daukar mutum biyu ko uku a kan babur dinsu, in kuma an ce su shiga da mutum lungu kada su shiga sai in sun yarda da dabi’un mutumin. Sannan muna rokon gwamnati ta kara kaimi wajen  ba mu tsaro. Muna kuma shawartar ’yan acaba baki su san inda za su rika shiga. Kuma za mu  kira  karamin taron kara wa juna sani don dada wayar da kan mutanenmu musamman wadanda ke bin wuraren da aka hana hawan babura.”

Wani mai sana’ar acaba da ke Unguwar Karofin Madaki mai suna Sani Mohammed Chindo ya ce a yanzu satar babur ta dauki sabon salo a cikin garin Bauchi musamman a daidai lokacin da wasu matasa suka rungumi sana’ar a matsayin ta dogaro da kai.

Sani Chindo ya ce a daidai wadansu baragurbin matasa na amfani da makamai wajen raunata masu acaba wanda in ya zo da karar kwana nan take sai a ji mutum ya mutu.

Ya ce, “A kan babur wallahi ba su dauki ran mutum a bakin komai ba, ganin yadda suke kashe mutum ko yi masa mummunan rauni. Wannan lamari na kashe ’yan acaba ya zamo ruwan dare a garin Bauchi inda zai yi wuya rana ya fito ta fadi ba a ji an kashe ko an raunata dan acaba an yi awon gaba da babur dinsa ba. Sabon salon da suka dauka shi ne mafi saukin satar babur wanda za a hura maka hoda ka rude. Mafi muni shi ne daba wa mutum wuka a ciki ko buga wa mutum guduma a kai. I Hakika wannan lamari ya zamo musifa,  Allah Ya yi mana maganin abin.”

Wadansu daga cikin ’yan acabar da Aminiya ta zanta da su sun ce wannan lamari yana matukar damunsu kuma suna kai rahoto ga jami’an tsaro kuma jami’an tsaron na bin kadinsu sai dai da yawa in an sace babur da wuya a sake samunsa, koda an yi bincike babur din ba ya dawowa.

Aminiya ta tuntubi mai rikon mukamin Jami’in Hulda da Jama’a na Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, ASP Alhassan Umar Magaji, inda ya ce ba za a ce wannan abu ya yi yawa sosai ba.

Magaji ya ce zai binciki irin wadannan zarge-zarge kuma, “Za mu kirawo ku mu yi muku bayani, amma ’yan sanda na iyakacin kokarinsu wajen magance aikata laifuffuka da kuma kare rayuka da dukiyoyin jama’a. Shi ya sa in ka lura ko dare ko rana za ka ga an baza ’yan sanda a dukkan lungu da sakon cikin gari da hanyoyin shigowa ko fita daga cikin garin, domin magance batagari,” inji shi.

Sai ya shawarci ’yan acaba cewa  duk lokacin da za su dauki fasinja in dare ya yi ya kamata su san inda za su shiga domin fitowa lafiya kuma su rika la’akari da irin mutanen da za su rika dauka da wuraren da za su kai su.