Mahukuntar Kwalejin Kimiya Da Fasaha ta Ibadan da ke jihar Oyo sun kone wayoyin salula na kimanin Naira miliyan 15 da su ka kwace daga hannun wasu daliban makarantar da ake zargin da harkalla a lokutan jarabawa.
Da yake wa manema labarai karin haske a lokacin da ya jagoranci aikin kone wayoyin salular a jiya Laraba mataimakin Shugaban Kwalejin Bayo Oyeleke ya shaida cewa a cikin shekara guda da ta gabata Hukumar makarantar ta kwace wayoyin daliban da ake zargi da satar jarabawa.
Ya kara da cewa, a dokar makarantar ba a yarda dalibi ya shiga dakin jarabawa da wayar salula ba dan haka sun dauki matakin kone wayoyin domin karfafa dokar tare da tsarkake sha’anin koyo da koyar wa a makarantar.