Da Dumi Dumi

Satar yara a Kano: Laifin mahukunta da iyaye ne

Masu iya magana kan ce, rana dubu ta barawo, rana daya ta mai kaya. Haka wannan karin magana Allah Ya tabbatar da ita a kan Mista Paul Onwe da matarsa, dukkansu ’yan kabilar Ibo mazauna birnin Kano a kwanakin baya, yayin da dubunsu ta cika a Kano kan sacewa da sayar da kananan yara da suka dade suka kuma kware a kai shekara da shekaru a wasu unguwannin kewayen birnin Kano. A tsakanin shekara 2016 zuwa 2017, mutanen unguwannin Birged da Kwana Hudu da Kawaji da Kawo da Tinshama da Walawai da sauransu, sun rika kokawa kan ana yawan sace musu kananan yara, al’amarin da zuwa wancan lokaci suka ce yaransu da aka sace sun kai 47.

A wancan lokaci da annobar ta addabe su, iyayen yaran da aka sace  har kungiya suka kafa da kan yadda za su iya tunkarar annobar a kungiyance. Duk da kafa kungiyar a duk lokacin da aka sace yaro sukan kai rahoto ga Rundunar ’Yan sandan Jihar, amma ’yan sanda ba su daukar maganar da muhimmancin da ya kamata, sai da ta kai jami’an ’yan sandan Kano suka kira shugabannin kungiyar suka yi musu barazanar kada su kara jin sun ce an sace musu yara. In kuma suka kara za su yaba wa aya zaki, wai ba gaskiya ba ce, so suke su bata sunan Kano da mutanenta.

Idan mai karatu bai manta ba, irin wannan hali na ko-in-kula da neman kauce wa gaskiya tsohon Shugaban Kasa Dokta Goodluck Jonathan da uwargidansa suka nuna lokacin da ’yan kungiyar Boko Haram suka sace ’yan matan Sakandaren Chibok a Jihar Borno su fiye da 200 a watan Afrilun 2014. A wancan lokaci Uwargidan Shugaban Kasar, har taro ta yi da Shugabar Makarantar da na Karamar Hukumar Chibok da Kwamishinan Ilimi na Jihar Borno da wadansu jami’an tsaro da shugabannin iyayen yaran a Abuja, inda ta rika yi musu tambayoyin soki-burutsu, na neman lallai su karyata satar ’yan matan. Haka mijinta ya yi ta jan kafa a kan matakan da ya kamata tunda zafi-zafin maganar gwamnatinsa ta dauka kan yadda za a ceto yaran. Ko a kwanan nan sai da tsohon Firayi Ministan Birtaniya Mista Dabid Cameron ya zargi Jonatahan kan ya ki amsa tayin da ya yi masa a kan yadda Birtaniya za ta ceto ’yan matan a cikin wani littafin da Mista Cameron ya fitar. Zargin da tsohon Shugaban Kasar ya musanta.

Kamar yadda sace ’yan matan Chibok din zuwa yanzu ya zama gaskiya da a yau ya cika kwanaki 2023 da aukuwa, haka satar yaran na Kano ya zama gaskiya, bayan da a ranar Laraba 11 ga Satumban da ya gabata, dubun Mista Paul da uwargidansa ta cika, lokacin da aka kama Mista Paul da wani karamin yaro mai suna Haruna Sagir Bako da ya sato daga Kawaji a kan hanyar tafiya da shi tashar mota zuwa Anacha na Jihar Anambra don sayarwa kamar yadda ya saba.

Bayan Mista Paul, ya shiga hannun ’yan sandan Kano ne, bincike ya sa aka hada da mai dakinsa inda aka wuce da su zuwa Anacha inda yake kai dukkan yaran da ya sata daga Kanon wajen dillaliyarsa,  Madam Ebere, wadda ta kan zabi na zaba ta ajiye a karkasahin kulawarta, saura kuma ta sayar ga mabukata. Kullum da sunan uwargidan Mista Paul da aka ce tana aiki a gidan marayu na Kano take samo kananan yaran, ma’ana dai iyayen yaran sun mutu. Daga baya Mista Paul da uwargidansa suka yi wa ’yan sanda rakiya zuwa yanzu, sun tabbatar dukkansu sukan sato yaran ne, yayin da shi Mista Paul ke kai su Anacha wajen Madam Ebere. Kuma ya ce yana  sayar da kowane yaro ko yarinya a kan Naira dubu 150 zuwa sama, gwargwadon hazakar da aka ga yaron yana da ita. Don an ce, a cikin yaran akwai wani masanin Alkur’ani da aka sayar fiye da Naira miliyan daya.

ADVERTISEMENT

Wancan zuwa da ’yan sanda masu bincike suka yi da shi zuwa Anacha, shi ya haifar da zuwa yanzu an gano yara takwasa can, kuma dukkansu ta hannun dillaliya Madam Ebere, wadda uku daga cikinsu a hannunta, sai Haruna Sagir Bako da sanadin satarsa a baya-bayan nan ta yi sanadiyyar  kama  Mista Paul.  Zuwa yanzu iyayen yaran da aka sace suna nan a kan bakarsu ta yara 47 aka sace masu tun daga shekarar 2014, lokacin da aka fara satar musu yara. Don haka saura yara 38, ke nan suka rage  wa’yan sanda su sake baza kaimi don ceto su. Mista Paul da mai dakinsa da mutum shida da ’yan sandan Kano suka samu kamowa daga Anacha suka taho da su Kano don ci gaba da bincike sun hada da dillaliya Madam Ebere, ta hannunsu ne a za ci gaba da neman sauran yaran.

Kodayake dukkan iyayen da aka kwato masu ’ya’yansu, ba wanda yake kukan ya ga dansa cikin wata mummunar kama ta tagayyara ko yunwa ko kishirwa ko wata azabtarwa, amma babban abin takaicin shi ne dukkan yaran an canja musu sunaye zuwa na kabilar Ibo da kuma addininsu, sun zama masu bin addinin Kirista sun bar Musulunci,  subhanallah!

Sannan sun fara koyon dabi’u da al’adun kabilar Ibo, al’amuran da ko a mafarki iyayen yaran ba su taba tunanin haka za ta taba kasancewa a cikin rayuwar ’ya’yansu ba. An ruwaito mahaifin daya daga cikin yaran yana kokawa kan yadda a yanzu dansa ba ya son yin Sallah, wata yarinya kuma iyayenta sun ce tana fargabar zuwa makarantar Islamiyya, kasancewar a hanyar zuwa Islamiyyar ce matar Mista Paul ta sace su ita da kawarta.

Bayan Gwamnatin Jihar Kano ta sha alwashin kafa kakkarfan kwamitin da zai bi kadin yadda aka sace yaran da yadda za a samu ceto sauran yaran da ba a iya ganowa ba da kuma tabbatar da an hukunta dukkan wadanda aka samu da hannu a cikin sace yaran da sauya masu al’adunsu da imaninsu. Ita ma Majalisar Dattawa ta sha alwashin bincikar al’amarin. Amma kafin a kai ga haka ya kamata iyaye su kara sanya idanu sosai a kan tarbiyyar ’ya’yansu dare da rana safe da yamma, don kuwa su Allah Ya dora wa amanar haka. Amanar da akasarin al’ummar Hausawa ba su tunawa da ita bare su san ta rataya a wuyansu, za ka iya fahimtar haka a kan yadda iyaye suke barin ’ya’yansu dare da rana suna yawo kwararo-kwararo, tamkar ba su da iyaye. Su ma jami’an tsaro lallai su rika sa tsoron Allah a cikin gudanar da ayyukansu na tsaron doka da oda da kare lafiya da rayuwa da dukiyoyin al’umma. Babbar cin amanar ’yan kasa ce ga ma’aikaci ya hakikice wajen boye gaskiya, don kawai ya kare nasa aikin. Lallai kowa ya rika tunawa shi makiyayi ne a kan abin da Allah Ya ba shi amana, kuma za a tambaye shi yadda ya tafiyar da abin da aka ba shi kiwo, kamar yadda Hadisin Manzon Allah (SAW) ya tabbatar.

Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya