✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Satar Yara: ‘Yan sanda sun gargadi iyaye da direbobi

Rundunar ‘yan sandan Legas ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a tashoshin mota wadanda suka hadar da ‘yan kungiyar direbobin mota da sauran…

Rundunar ‘yan sandan Legas ta yi kira ga masu ruwa da tsaki a tashoshin mota wadanda suka hadar da ‘yan kungiyar direbobin mota da sauran al’ummar gari,  su dinga sanya idanu a kan matafiya da ke dauke da yara wadanda ake da shakku akan su.

Kakakin rundunar ‘yan sandan Legas DSP Bala Elkana, ne ya yi kiran a takardar da ya fitar bayan da jami’an ‘yan sandan sun kame wata mata da mijinta da ake zargi da sato wasu yara biyu daga garin Jos a lokacin da suke yunkurin tafiya da yaran garin Onitsha a jihar Anambra.

Ya ce, a ranar Alhamis din da ta gaba ta ne aka kame matar a wata tashar motoci da ke daura da kasuwar duniya ta Alaba a daidai lokacin da take yunkurin tserewa da yaran zuwa garin Onitsha, yara biyu maza masu suna Joshua James Mai shekara 6 da Samuel  Gbawune mai shekara 3,” Matar mai suna Chukwunonso Blessing, mai shekaru 30 ta shaida cewa mijinta ne ya sato yaran daga wani gidan marayu a garin Jos inda ya bata su ta kai su Onitsha.” In ji shi.

Ya ce, an kame mijin matar mai suna Chukwunoso Happiness, mai shekaru 40 wanda ya shaida cewa ya sayi yaran ne akan Naira dubu 140 a garin Jos a wajen wata mata mai suna Mama Oyoo, DSP Bala Elkana, ya kara da cewa zuwa yanzu an kubutar da yaran kana ana bincike domin gano iyayen su.