✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Satar zati a kafafen sadarwa na zamani (16)

Matashiya Idan masu karatu na tare da mu, mun fara bayani kan hanyoyin kariya daga masu satar zatin mutane. Kafin wannan lokaci mun dauko bayani…

Matashiya

Idan masu karatu na tare da mu, mun fara bayani kan hanyoyin kariya daga masu satar zatin mutane. Kafin wannan lokaci mun dauko bayani tiryan-tiryan kan wannan mummunar ta’ada, inda muka fara da bayani kan ma’anar satar zati da dalilan da suka sa barayin zati ke satar bayanan mutane da kuma na’uka ko fuskokin da wannan nau’in ta’addanci ke dauka. Yadda ake satar mutane a zahirin rayuwa, haka ake satar mutane a shafukan sada zumunta. Illa dai bambancin da ke tsakani shi ne: a zahirin rayuwa ana sace mutum ne gaba dayansa da gangar-jikinsa da ruhinsa. Amma a shafukan sada zumunci, ganin cewa ba zahirin gangar-jiki ba ne ke bayyana a shafukan, ana sace zatin mai shafin ne.

Satar zati a kafafen sada zumunta na daukar fuskoki mabambanta. Akwai wanda za a sace zatinsa, ana gudanar da abubuwa da sunansa, amma bai sani ba. Haka wadanda ke mu’amala da barawon su ma ba za su gane cewa ba wanda suke zato ba ne. Watakila saboda bai cika mu’amala da shafin ba a-kai-a-kai. Idan haka ta faru, barawon na iya tura wa abokan mai shafin sako cewa yana matukar bukatuwa zuwa ga kudi, su taimaka masa. Kasancewar sun san shi, ba za su yi wani dogon bincike ba, musamman idan na kusa da su ne. A yanayi irin wannan barawon kan canja “Password” din mai shafin ne, don hana shi hawa, balle ya ga irin wainar da yake toyawa.

Fuska ta biyu ita ce, ana iya sace zatin mai shafi amma a ki canja “Password” dinsa. Barayin da ke amfani da wannan tsari suna yin haka ne don sauraro ko gani ko leken asirin mai shafin, don ji da gani da kuma kwasan irin bayanan da yake aikawa ko karba. Wannan na faruwa a dandalin Facebook da Twitter da kuma Imel. Barawon zai yi ta lura da mai shafin ne, tare da nadar irin bayanan da yake so, ba tare da mai shafin ya sani ba balle ya canja “Password” dinsa.

Fuska ta uku kuma, ana iya sace zatin mai shafi a dandalin abota ta hanyar kwafar bayanansa da hotunansa da lambar wayarsa, da sunansa da duk wani abin da zai iya taimakawa wajen kwaikwayon rayuwarsa, sai a bude shafi makamancinsa. Wannan shi ne mafi muni daga cikin hanyoyin satar zatin mai shafi. Domin da wannan tsari, ana iya yaudarar mutane da dama wadanda suke aminai ne ko ’yan uwan wanda aka saci zatinsa. Cikin makonnin baya na ga wata ’yar uwa ta aika wa wata ko wani sako ta Inbod, tana rokonsa ko rokonta da ya cire sunanta da hotonta da ya sa a “Profile” dinsa ko dinta, sannan ya ji ko ta ji tsoron Allah ya ko ta rufe shafin nan. Da na duba sai na ga da irin sunanta ne aka bude shafin da shi, sannan hotonta ne sak a dore a kan “Profile” din shafin. Wani karin abin takaici ma shi ne, barawon da ke amfani da wannan tsari yana iya tura wa abokanka sako, cewa su karbe shi a matsayin aboki, ya samu matsala ne da tsohon shafinsa. Mai amfani da wannan fuska wajen satar zatin mutane a dandalin abota har wa yau, kan aikata badakala nau’uka daban-daban da sunan mai shafin, ta hanyar bin wadanda yake tunanin sun san mai sunan, yana zambatarsu. Na yi rubutu a shekarar 2015 a shafina da ke Facebook, don fadakar da jama’a kan wannan matsala. Musamman dangane da mutanen da ke bude shafuka da sunan manyan shugabanninmu, na da ko na yanzu – irin su Atiku Abubakar da Shugaban Kasa mai ci da Abdullahi Dikko Inde da Mai martaba Sarkin Kano Amir Muhammad Sanusi II –  don yaudarar jama’a. Wannan duk matashiya ce; ina fata wadanda ke tare da mu tun farkon wannan silsila sun fahimci tsarin.

Kasancewar galibin dalilin da ke haddasa satar zati na aukuwa ne ta hanyar “Password”, ya sa muka fara da bayani kan yadda “Password” yake – ma’anarsa da nau’ukansa da siffofinsa da kuma ka’idoji ko dokokin zabar “Password”. Daga wannan mako in Allah Ya so, za mu duba sauran bangarori ko dalilan da ke sauwake wa Dan Dandatsa satar zatin mutane. Wadannan jerin kasidu dai su ne bangaren karshe na wannan silsila da muka faro wajen watanni biyu ko uku da suka gabata.

 

Hanyoyin kariya (2)

A baya, sa’ar da muke bayani kan hanyoyin da ’yan Dandatsa ke bi wajen tattaro bayanan jama’a, bayan na sata, akwai wadanda suka shafi bayanan da suke tsinta a bola da wadanda suke tsinta a bolar Intanet da wadanda suke tsinta a tsofaffin kayayyaki da na’urorin sadarwa – irin su Kwamfuta da Router da Flash da Zip Dribe da sauransu. Kasancewar ire-iren wadannan hanyoyi – idan ke kebance tsofaffin kwamfutoci da mutum zai iya saya a hannun wani ko daga wata ma’aikata – ba su shahara a wannan bangaren da muke rayuwa ba, za mu shagaltu da hanyoyin suka yadu ne kawai. Sauran kuma a hankali idan sun fara bayyana a nan, sai mu dube su sosai.

 

Tsofaffin kayayyaki da na’urorin sadarwa

Idan kana da tsohuwar kwamfuta da kake son sayarwa ko bai wa wani kyauta, yana da kyau ka yi mata wanka da wanki. Ba wai ina nufin ka nemo ruwa da muke sha ka wanke ta da su ba. Ina nufin ka kwashe duk abin da ke ciki, ka cire dukan wata manhaja da kasan ka taba shigar da adireshinka na Imel da kuma “Password” a ciki. Hatta manhajar lilo wato: “Browswer;” idan ba ka iya share bayanan da ke kanta na shafukan Intanet din da ka hau ba, ka cire ta kawai (Uninstalling) daga kan kwamfutar. In da hali, kawai ka yi “Resetting” ko “Reformatting” kwamfutar kawai; ta koma sabuwa ta bangaren ruhi, kamar yadda ake kera ta. Idan kuma ma’adanar Flash (Flash Dribe) kake son kyautarwa, ita ma ka goge duk abin da ke kai.

 

Taka-tsantsan da bayanan Imel

Duk da cewa da yawa cikinmu ba mu cika damuwa da yin rajistar Imel ba, idan ba tilasci ba ne irin ta aikin gwamnati, ko makaranta, ko wani abu makamancin haka, ga masu akwatin Imel, dole ne su rika taka-tsantsan da bayanansu. Idan kana amfani da Imel a shafinka na sada zumunta, to, ka san cewa “Password” dinka na Imel ya fi muhimmanci a kan “Password” dinka na Facebook ko Twitter. Domin duk wanda ya samu “Password” dinka na Imel, wanda ka dora a shafinka na Facebook, sace shafinka gare shi ba abu ba ne mai wahala. Duk wanda ya bukaci adireshinka na Imel, adireshin kadai za ka ba shi, ban da “Password” din. Shi “Password” sirrinka ne a duniyar sadarwa. Duk wanda ka ba shi “Password” dinka, to, ka bude masa sirrinka ne gaba daya. Wadansu ba su bambancewa, idan ka ce “Ba ni adireshinka na Imel” sai ya cillo maka har da “Password” din.  Wannan kuskure ne, don haka a kiyaye.

 

Taka-tsantsan da bayanan shafukan sada zumunta

Idan kana da shafi a Facebook ko Twitter ko Youtube ko LinkedIn, dole ne ka rika taka-tsantsan da su; kada ka taba ba wani “Password” dinka na Facebook ko daya daga cikin wadannan shafuka sai da hujja kwakwara. Watakila wani ya sace maka shafinka, ana kokarin ceto shafin, kuma kai ba za ka iya ba. To a nan ba laifi ka bai wa masanin da zai ceto shafin. Domin a yanzu “Password” din, in ma yana da wani amfani, to amfaninsa kadan ne. Da zarar an gama gyara shafin ko kwato shi, koda wanda ya gyara shafin ya sanya maka sabon “Password”, ka yi maza ka canja naka. Sannan ka sani, ba a ba da aron “Account” ko shafin Facebook. Da yawa cikin mata kan ba da aron account, nasu na kansu ga kawayensu. Wannan kuskure ne. Munanan labaru kan haka na nan birjik, sai a kiyaye.

 

Taka-tsantsan wajen bayar da bayanai a gidajen yanar sadarwa

Ga wadanda ke shawagi a gidajen yanar sadarwa na Intanet don neman fa’idoji kan bincike ko fadakarwa ko karin bayani, galibi idan ka bukaci wasu bayanai a wasu shafukan gidajen yanar sadarwa, akan bukaci ka yi rajista tukun, kafin ka samu damar shiga. Wannan rajistar galibi ba ta wuce ka bayar da adireshinka na Imel, sannan ka zabi “Password.” Da wadannan bayanai ake sa ran nan gaba idan ka sake ziyartar gidan yanar, za ka yi amfani wajen shiga ko isa ga shafin da kake bukata. Bayan adireshin Imel, akan bukaci ka bayar da sunanka, da a wasu lokuta ma da adireshin inda kake zaune. Wadannan bayanai naka suna da muhimmanci a gare ka, kuma sau tari ire-irensu ne Dan Dandatsa ke bukata don kera jabunka. A nan sai ka kiyaye. In so samu ne, ka yi rajistar adireshin Imel na musamman, wanda shi za ka rika bayarwa idan an bukata, kuma da shi za ka rika karbar sakonni ko bayanan da kake bukata a ire-iren wadannan shafuka. Ya zama adireshin Imel ne na jeka-na-yi-ka kawai.

Amma asalin adireshinka na Imel, wanda ke wakiltar sahihan bayananka, ka ajiye shi don bukata ta musamman. Haka ma suna, ya zama kana da wani lakabi da za ka rika amfani da shi a ire-iren wadannan muhalli. Idan adireshi ne ma, ka rika amfani da takaitattun bayanai. Amma hakikanin bayanan da suka shafe ka kai-tsaye, ka kebance su ga lokaci da yanayi da kuma muhalli na musamman. Misali, ina da adireshin Imel wanda da shi nake karbar sakonnin masu karatu a wannan shafi. Ina da adireshin Imel wanda da shi nake gudanar da cinikayya a shafukan Intanet, ina kuma da adireshin Imel wanda shi nake bayarwa a gidajen yanar da na je neman bayanai. Haka ma suna, ba na amfani da hakikanin sunana, ko hakikanin adireshina, ko kuma hakikanin Imel dina, a ko’ina. Wannan misali ne.