✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Satar zati a kafafen sadarwa na zamani (19)

Idan Matsala ta Auku: A baya na bayyana cewa a kasashen Turai da Amurka, da zarar an sace zatinka har ta kai an aikata ta’addanci,…

Idan Matsala ta Auku: A baya na bayyana cewa a kasashen Turai da Amurka, da zarar an sace zatinka har ta kai an aikata ta’addanci, kuma jami’an tsaro suka fara nemanka, to aiki ja ya same ka, inji mutanen Danja da ke Katsina. Kamar yadda a yanzu a Najeriya, Allah kiyaye Ya kuma tsare, a sace wa mutum katinsa na ATM, ko katin shaidar zama dan kasa (National ID Card), ko bayanan da yake amfani da su wajen aiwatar da cinikayya a shafuffukan Intanet, har a je a aikata ba daidai ba da su, da zarar jami’an tsaro sun gano wannan badakala, ba wanda za a nema sai kai. Ko kuma wani ya sace bayananka na Facebook, misali ya haye shafin ya rika aikata shegantaka a kai, har jama’a su fara kiranka suna tambayar me ke faruwa ne? Mun ga kaza da kaza a shafinka. Idan irin haka ta faru, mene ne abin yi?

Da farko dai, kamar yadda na sanar a baya, a Najeriya babu wani tsari na musamman da aka samar kan ire-iren wadannan matsaloli, ta la’akari da irin muhallin da suke faruwa. Amma akwai wasu tsare-tsare na al’ada da dokar kasa ta tanada don magance haka. Na farko idan ya shafi taskarka na banki ne, kana iya sanar da bankinka kai-tsaye, cewa an sace katin ATM dinka, ko an kwace daga hannunka, ko kuma an sace bayanan da ke cikin katin, ko kuma an sace bayanan da kake amfani da su wajen hawa shafin da ke dauke da taskar ajiyarka na banki, kuma an aiwatar da cinikayya ko cire kudi ko wani abu makamancin haka, ba tare da sani da kuma yardarka ba. Nan take bankin zai kulle wancan kati naka. Idan an ciri kudade daga taskar kafin ka farga, ya danganci daga inda sakacin ya samo asali.  Idan ta bangarenka ne, to, wannan kai za ta shafa kai-tsaye. Idan kuma ta bangaren bankin ne aka samu wannan sakaci (wanda gano hakan gare ka zai yi wuya, kuma su ma zai yi wuya su gaya maka gaskiya idan su ne abin ya shafa), su za su dauki dawainiyar biyanka amma fa sai ka dage.

Idan kuma ta’addanci aka aiwatar da katin naka, wanda ya shafi kisa ko fashi da makami ko sata ko wani abu makamancin wannan, to, a nan kam wajen jami’an tsaro za ka tafi kai-tsaye. Idan ka sanar da su abin da ke faruwa, za su ba ka takarda ta musamman ka cike, mai dauke da sanarwar cewa abu kaza ya faru da kai a rana kaza a wuri kaza. Wannan zai taimaka wajen ba ka kariya ko da nan gaba wadansu sun zo suna cewa kai ne ka aiwatar da wannan aika-aika a kansu, sanadiyyar shaidar da suka gani na katinka ko wasu bayanai masu alaka da kai kai-tsaye. Sannan har wa yau za ka je kotu ka yi rantsuwa, cewa abu kaza din nan da ka gaya wa jami’an tsaro cewa ya faru, lallai gaskiya ne ba karya ba. Wadannan takardu biyu su za su taimaka wajen ba ka kariya nan gaba da kuma taimaka maka wajen samun sabon kati ko shaidar da ka rasa, sanadiyyar waccan sata ko ta’addanci da aka yi a kanka.

Idan kuma shafi ne a dandalin sada zumunta, nan kuma garzayawa za ka yi wajen dakile hakan. Idan an sace shafin ne, ta yadda ba ka iya hawa, to, dole ne ka bude wani shafi, ko ka sa abokanka su rubuta a kan farfajiyar shafin da aka sace, cewa duk rubutun da ke bayyana a wannan shafi daga rana kaza, ba kai ba ne kake rubutawa. Maimakon haka ma, an kwace maka shafin ne, ba ka iya sarrafa shi. Don haka, a yi hattara; kada wani yayi alaka da wanda ke sarrafa shafin ta kowace hanya. Har wa yau, idan wanda ya kwace shafin yana aikata wasu abubuwa da suka shafi ta’addanci ne ga al’umma, na zance ko na aiki, to, dole ne ka sanar da jami’an tsaro cewa ga abin da ke faruwa. Kada ya je ya aikata abin a aikace, a zo ana nemanka.

Kammalawa:

Daga bayanan da suka gabata, na tabbata mai karatu ya fahimci abubuwa da dama kuma ya dauki darasi. A kullum ka zama mai taka-tsantsan wajen mu’amala da mutanen da ba ka taba saninsu ba a shafukan Intanet. Ka sani, kana da mutunci, da yake dole ka kare.  Kana da addini, da ya zama dole ka kare shi. Kana da al’adu kyawawa, da suka zama dole ka ba su kariya. Kana da iyali, da ya zama dole ka mutunta su.  Kana da ’yan uwa da dangi da iyaye, da suka zama dole ka karrama su ta hanyar kauce wa duk wata barna da za ta iya janyo musu abin kunya.

A kullum masu neman aikata barna ba su gajiya, kuma iya tausayinka gare su, iya yadda za su shige ka. Don haka wajibi ne ka zama mai taka-tsantsan wajen irin mu’amalar da kake da duk wanda ba ka san shi ba, ko wanda ka sani amma ba natsattse ba.