✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sau biyu ina bari saboda dukan da mijina yake mini -Simbiat Saula

Wata matar aure mai suna Simbiat Saula ta kai mijinta kara kotun gargajiya da ke yankin Ikorodu a Jihar Legas tana neman a raba aurensu…

Wata matar aure mai suna Simbiat Saula ta kai mijinta kara kotun gargajiya da ke yankin Ikorodu a Jihar Legas tana neman a raba aurensu da mijinta Muyideen kan zargin dukan da yake mata.
Simbiat, mai kimanin shekaru 27 da ke zaune a unguwar ta Ikorodu, kuma ’yar kasuwa ce, ta bayyana wa kotun cewa saboda dukan da mijinta yake mata akai-akai, sau biyu tana barin ciki.
“Kusan kullum sai ya dake ni. Ba shi da yarda. Abu kadan, sai ya rika zargina da bin maza. Saboda duka sai da cikina ya zube har sau biyu. Ina neman kotu ta raba aurenmu. Ba na bukatar ci gaba da zama da shi, gara na je na auri wanda zai zauna da ni lafiya”. Inji ta.
Shi ma Muyideen, mai kimanin shekaru 40, ya amince kotun ta raba aurensu, amma ya musanta zargin duk, sai dai ya zarge ta da bin maza suna sheke aya a wuraren shakatawa. “karya take yi, ban taba dukanta ba. Abin da take yi, ko mahaifiyarta ta sani, kullum dare sai ta amsa wayar mazan da take yin lalata da su. Har bude kafa ta yi a kafar sadarwa ta ‘Facebook’ inda take tattaunawa da samarinta. Tana shirya inda za su hadu. Ni da ma na gaji, na rasa yadda zan yi”. Inji shi.
Alkalin kotun, Mista Emmanuel Daniel da ya saurari bayanansu, ya dage ci gaba da sauraron karar zuwa ranar 31 ga watan gobe.