✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Saudiyya ta bai wa Albashir miliyoyin daloli’

Tsohon Shugaban Sudan Omar Albashir ya amshi miliyoyin daloli daga Saudiyya inji wani jami’in tsaro a kotun Sudan. Tsohon Shugaban ya bayyana a gaban kotu…

Tsohon Shugaban Sudan Omar Albashir ya amshi miliyoyin daloli daga Saudiyya inji wani jami’in tsaro a kotun Sudan.

Tsohon Shugaban ya bayyana a gaban kotu ne a farkon makon nan, inda ake zarginsa da karbar rashawa, zargin da lauyoyinsa suka musanta.

An hambarar da shi ne a watan Afrilun bana, bayan ya kwashe kusan shekara 30 a kan mulki.

A watan Yunin bana ne mahukuntan kasar suka ce an samu miliyoyin daloli cikin buhuna a gidansa.

A ranar Lahadin da ta gabata ce aka cimma yarjejejiniya domin kafa gwamnatin hada-ka a tsakanin sojoji da farar hula.

Ana zargin tsohon Shugaban ne da samun “kyautuka ta haramtacciyar hanya da kuma “mallakar kudaden kasashen waje.”

A watan Afrilun da ya gabata, Shugaban Sojojin da ke mulkin kasar, Abdel Fattah al-Burhan, ya  ce sun gano kimanin Dalar Amurka miliyan 113 daga gidan Al Bashir.

Sai dai lauyoyin da ke kare tsohon Shugaban, sun musanta zargin da ake yi masa.

Tun farko dai, an yi shirin gurfanar da shi ne gaban kotu a watan Yuli; amma saboda dalilan tsaro  aka dage gurfanar da shi.

Akwai wani zargin?

A watan Mayu ne dai Babban Lauyan Gwamnatin Kasar ya bayyana cewa sun kai karar Al Bashir a kan iza wutar zanga-zanga da kuma sa hannu wajen kisan masu zanga-zangar kin jinin mulkinsa.

Zargin da ake yi masa ya biyo bayan wani bincike ne a kan mutuwar wani likita, wanda aka kashe lokacin zanga-zangar, abin da ya yi sanadiyyar kawo karshen mulkin Al Bashir a watan Afrilu.

Wani ganau ya bayyana wa BBC cewa duk da cewa likitan ya daga hannayensa yana yi wa ’yan sanda bayanin cewa shi likita ne; amma sai da suka harbe shi.