✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saudiyya ta dawo da ‘yan Najeriya 292 gida

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da isowar ‘yan Najeriya 292 da suka makale a kasar Saudiyya sakamakon dokar kulle. Jirgin da ya kwaso mutanen, wadanda galibinsu…

Gwamnatin tarayya ta tabbatar da isowar ‘yan Najeriya 292 da suka makale a kasar Saudiyya sakamakon dokar kulle.

Jirgin da ya kwaso mutanen, wadanda galibinsu dokar kulle a kasar ce ta tilasta musu dawowa gida, ya sauka a filin jiragen sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ranar Talata.

Ministan Harkokin Waje na Najeriya, Geoffrey Onyeama, wanda ya sanar da saukar tasu a shafinsa na Twitter ranar Laraba, ya kuma ce akasarinsu mata ne masu shayarwa da kuma kananan yara.

“Jiya Talata muka karbi mutum 292 da gwamnatin Saudiyya ta kawo mana su kuma sun sauka a filin jiragin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

“Dukkansu suna nan mun ajiye su a dakunan otal inda za su zauna a killace har tsawon makonni biyu kamar yadda hukumomin lafiya suka ba da shawara”, in ji ministan.

Cutar coronavirus dai ta tilasta wa kasar ta Saudiyya wadda daya ce daga cikin kasashe masu arzikin man fetur a duniya kulle iyakokinta da kuma kara harajin da ake biya a kan kayayyaki wato VAT don gani ta farfado da tattalin arzikinta.

Hakazalika, cutar ta tilastawa kasar rufe kusan dukkan biranenta, cikin har da biranen Makkah da Madinah wadanda Musulmi ke ziyarta don ayyukan ibada.

A cikin makonni biyu da suka gabata dai Najeriya ta kwaso mutanenta da dama daga wasu kasashen duniya wadanda akasarinsu dokar kulle ta tilastawa dawowa gida.