Subscribe
  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin
Saudiyya ta zamanantar da jifar Shaidan

Saudiyya ta zamanantar da jifar Shaidan

Kasar Saudiyya ta shigo da sabon tsari na zamani wajen jifar jamrori uku da ke Muna (jifar Shaidan), wanda akan gudanar bayan hawan Arfa.

Kasar ta dauki wannan mataki ne domin lura da zirga-zirgar mahajjata tare da tabbatar da bin doka domin kare aukuwar turmutsitsi a lokacin aikin Hajji.

A watan Satumban shekarar 2015, an kiyasta cewa turmutsitsin da aka samu a wurin jifar Shaidan ya haifar da rasuwar mutum 2000.

Yawan mutanen da aka rasa a wancan lokacin shi ne mafi muni a tarihin aikin Hajji da Musulmin duniya ke yi a kasar Saudiyya.

Wakilin Hukumar Hajji ta Najeriya a Saudiyya, Alhaji Tanko Aliyu, ya ce bukatar samar da wannan sabon tsari ta taso ne ganin cewa an sha samun matsaloli wurin jifar Shaidan a shekarun baya, inda a wasu lokuta wadansu alhazai kan bace a lokacin jifar.

Jifar Shaidan dai na daga cikin muhimman ayyukan aikin Hajji.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) ya ambato Alhaji Tanko Aliyu yana cewa, za a rika kai alhazan Najeriya zuwa wurin jifa rukuni-rukuni, a lokuta daban-daban da za su gudanar da nasu jifar.

Sannan an tanadar da hanya ta musamman da alhazan Najeriya za su bi zuwa wurin jifar, kasancewar Najeriya ce ke da kashi daya cikin uku na alhazai bakaken fata da za su gudanar da aikin Hajjin na bana.