✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Saukan ruwan sama da wuri na yin barazana ga gonakin tumatir a Katsina – Manoman Rani

Manoman rani a Jihar Katsina sun nuna damuwarsu kan ruwan saman da aka fara samu a jihar, ganin yadda ya jawo suka tafka asara musamman…

Manoman rani a Jihar Katsina sun nuna damuwarsu kan ruwan saman da aka fara samu a jihar, ganin yadda ya jawo suka tafka asara musamman a bangaren noman tumatir.

Ruwan sama na farko kafin shigowar damina yana haifar da matsanancin zafi da ke lalata yabanyar tumatir inda take haduwa da matsalolin da suke illa ga tumatirin da aka shuka.

Malam Muhammad Saminu Dantankari ya ce, ba su rokon Allah Ya saukar da ruwa a wannan lokaci da muke tsakiyar noman rani.

“Noman rani lokacin zafi ne ake yin sa a yanayin da kasa ta dauki dumi hakan shuka ke so ta girma nan take, kana yi mata ban ruwa yadda take so, a haka sai ka samu nasarar nomanka, amma ruwan sama hadari ne ga shukar rani, zai samar da matsanancin zafi da shukar ba ta iya jimirinsa sai a ga ta langwabe,” inji shi.

Ya kara da cewar ba abin da za su yi ga wannan yanayi da ya wuce addu’a, inda ya ce mafi yawan manoman suna haduwa da tarnaki a noman ranin tun farkon watan Nuwamban bara, kuma masu noman tumatir ne suka fi haduwa da wannan jarrabawar.

Shi kuwa Shehu Abdullahi mai shekara 28 cewa ya yi, sun yi farinciki ruwan saman da aka yi bai yi karfi sosai ba, da zai iya barnata amfanin gonarsu.

“Mun yi nasara muna fatan ruwa ba zai dawo ba muna kan addu’a kada ya dawo sai zuwa watan Afirilu ko Mayu don mu samu lokacin girbe amfanin gonarmu,” inji shi.

Ya ce nau’o’in tumatir da ake da su akwai mai son ruwan sama a nomansa, irin tumatir na UTC kuma ba ya bukatar ruwan, zai iya lalacewa in ruwan ya kwanta a jikinsa.

Abdullahi ya nemi manoma su rika kula da lissafin lokacin nomansu a koyaushe tare da la’akari da canjin yanayi don rage asarar noman raninsu.

Kabiru Yusuf Sanyinna a Sakkwato shi ma ya bayyana jin tsoronsa ga ruwan fari kafin shigowar damina, wanda ya ce yana lalata amfanin gonarsu gaba daya. Fatarsa Allah Ya yi musu mafi alheri a bana.

Wannan rahoton ya fahimci mafi yawan manoman tumatir sun kai matakin cire amfanin gonarsu, kuma a kasuwar tumatir ana samun karamin kwando a kan Naira 600 zuwa 800, babba  kuma Naira 1,800 zuwa Naira 2,400 ya danganta da kyan tumatirin.