✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

…Sauran shugabanni ma sun yi tafiye-tafiye

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo a nasa bangaren, ya yi tafiye-tafiye zuwa kasashe 97, inda ya kwashe kwanaki 139 a kasashen da ya je tsakanin…

Tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo a nasa bangaren, ya yi tafiye-tafiye zuwa kasashe 97, inda ya kwashe kwanaki 139 a kasashen da ya je tsakanin shekarar 1999 da ya hau mulki zuwa shekarar 2007 da ya bar karagar mulki.

Daga cikin kasashen da ya je akwai Indiya, inda ya je a watan Janairun shekarar 2000, sannan ya je Koriya ta Kudu a watan Yuli na shekarar. Sannan ya je kasar Indonesiya a watan Oktoban shekarar 2007.

Bayanai sun nuna cewa ya fi zuwa kasar Amurka, inda ya je kasar sau 8 a zamanin mulkinsa.

Marigayi Shugaba Umaru Musa ’Yar’adua kuwa ya sha fama da jinya, inda ya dauki tsawon lokaci a kasashen waje yana jinya. Daga cikin kasashen da ya je akwai Amurka da Jamus da Saudiyya da Brazil da sauransu.

Shi kuwa tsohon Shugaban Kasa Goodluck Jonathan, wanda ya yi mulki a tsakanin shekarar 2010 zuwa 2015, ya je kasashe da dama, ciki har da Amurka da ya je sau uku. Sannan ya je kasashe irin su Faransa da Ghana da Chadi da Brazil da Uganda da sauransu.

A kasafin kudin shekarar 2013, ya kasafta kashe Naira biliyan 2.6 domin tafiye-tafiye.

Shi kuma Shugaba Buhari, daga hawansa mulki a shekarar 2015 zuwa yanzu, ya je kasashe 40, inda ya kwashe kwana 407. Daga cikin kasashen da ya je akwai Birtaniya da Amurka da Saudiyya da Faransa da China da Kenya da Mali da sauransu.

Ya fi dadewa a kasar Birtaniya, inda ya kwashe kwana 217. Sai kuma kasar Amurka da ya yi kwana 41, sai Saudiyya da ya yi kwana 18 sai kuma Faransa da ya yi kwana 11.

Daga cikin kasashen da ya je akwai kasashe biyar da ya yi kwana dai-daya, kamar Burkina Faso da Gambiya da Mali da Nijar da Laberiya.