Da Dumi Dumi

Saurayi ya kashe wanda ya haska budurwarsa da fitila a Kano

Ankwa

Wani saurayi mai shekara 22, mai suna Ibrahim Magaji da ke kauyen Kosawa, a Karamar Hukumar Kura ta jihar Kano, ya rufe wani mai suna Auwalu Hussaini da duka wanda hakan ya yi sanadiyyar rasuwarsa, saboda ya haska budurwarsa da fitila.

Ibrahim, ya ziyarci gidan su budurwarsa ne wanda aka sakaya sunanta a Kauyen Dakasoye da ke cikin Karamar Hukumar Garum Malam ranar Lahadin da ta wuce.

Aminiya ta gano cewa, wanda ake zargin da kashe Auwalu, yana tsaye ne tare da budurwarsa a lokacin sai Auwalu, ya haska budurwar.

Jami’in hulda da jama’a na Rundunar ‘yan sandar jihar DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya tabbatar da kama wanda ake zargin da aikata kisan.

Auwalu, ya rasu ne a babban asibitin garin Kura.

ADVERTISEMENT
Tura
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya