✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sauya shekar gwamnonin ba zai sa su sauka daga kujerunsu ba- Lauya Aturu

Fitaccen lauya kuma mai rajin kare hakkin dan Adam da ke Legas, Barrista Bamidele Aturu ya ce sauya sheka da gwamnonin sabuwar PDP suka dauka…

Fitaccen lauya kuma mai rajin kare hakkin dan Adam da ke Legas, Barrista Bamidele Aturu ya ce sauya sheka da gwamnonin sabuwar PDP suka dauka ba zai shafi kujerunsu ba.
Lauya Bamidele Aturu ya shaida wa manema labarai cewa “Babu dokar da ta nuna cewa idan Gwamna ya sauya sheka zuwa wata jam’iyya ya yi asarar kujerarsa. Idan dan majalisa ne ya sauya sheka zuwa wata jam’iyya to shi doka ta nuna cewa ya yi asarar kujerar. Dole ya sauka daga kan mukaminsa. Saboda haka gwamnonin suna nan daram a kan mukamansu na gwamnonin jihohinsu.”
Wani matashin dan siyasa da ke Legas, Alhaji Salisu Buly ya yaba da matakin da gwamnonin suka dauka na komawa Jam’iyyar APC.
Ya ce “Sun yi daidai kuma sun dauki matakin da ya dace. Da ma mun dade muna jiran su yanke hukunci. Saboda haka muna goyon bayansu dari bisa dari. Kuma muna tabbatar musu cewa mu matasa muna tare da su. Sai dai ina so na jawo hankalinsu su ji tsoron Allah kada su ba mu kunya domin mun fara jin wasu gwamnonin sun fara lashe amansu. To muna kira su dubi talakawan da suke jagoranta su taimaka a kawar da gwamnatin Jonathan a zaben shekarar 2015. Muna yaba wa Gwamna Kwankwaso da sauran gwamnonin da suka amince da matakin.”