✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

SERAP ta ba Buhari kwana 7 ya bayyana kadarorinsa

Kungiyar Tabbatar da Adalci a Al’amuran Mulki (SERAP), ta bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo da gwamnoni da mataimakansu, su bayyana…

Kungiyar Tabbatar da Adalci a Al’amuran Mulki (SERAP), ta bukaci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo da gwamnoni da mataimakansu, su bayyana dukiyar da suka mallaka cikin kwana bakwai.

Kungiyar SERAP ta bukaci bayyana dukiyar manyan jami’an gwamnatin ne da suka mika ga hukuma da Kotun Da’ar Ma’aikata kamar yadda doka ta tanada.

Kungiyar ta ce ta nemi bayanin ne bisa dokar ’yancin samun bayanai; tana mai cewa rashin bayyana kadarorin a fili ba ya taimakon gaskiya da amana.

SERAP ta ce, bayan cikar wa’adin, matukar jami’an ba su bayyana dukiyar tasu ba, za ta dauki matakin da ya dace don tilasta su, su bayyana.

Shugaba Buhari ya sha suka kan rashin bayyana dukiyarsa lokacin da ya hau mulki a 2015, inda daga baya ya fito da bayanan dukiyar ta sanarwar da Kakakinsa Malam Garba Shehu ya faitar.

A wannan karo bayan dawowarsa mulki a bara, bayanin ya nuna ba wani sauyi da aka samu a dukiyar Shugaba Buhari don bai bude wasu asusu a bankuna ba.

A bayanan da ake da su, Mataimakinsa Osinbajo, ya fi shi dukiya.

A kowanne lokaci jami’an Shugaba Buhari na nuna tara dukiya ba ta gaban Shugaban.

’Yan adawa na caccakar Shugaban cewa yana da dabarun boye abin da ya mallaka ko na ’yan uwa da iyalansa.

Alhaji Buba Galadima ya fito da wani zargi da ya shafi gidan Shugaban duk da dai fadar Shugaban ta yi watsi da zargin.

Duk da matsin lambar SEPAP ga Kotun Da’ar Ma’aikata, ta ki bayyana dukiyar Shugaban da sauran jami’an zartarwa da nuna doka ba ta ba ta damar haka kai-tsaye ba.