Da Dumi Dumi

Serena Williams ta kamu da ciwon baya a daidai lokacin da take buga wasan karshe

Shahararriyar ’yar wasan kwallon Tennis ta duniya da ke Amurka Serena Williams ta kamu da ciwon baya a daidai lokacin da take yin wasan karshe da wata ’yar kasar Kanada a gasar cin Kofin Tennis na 2019 Rogers Cup a ranar Lahadin da ta gabata.

Williams tana karawa ne da Bianca Andreescu kuma ita ke kan gaba da ci 3-1 sai ciwon baya ya kamata inda hakan ya sa ta hakura da gasar kuma ta amince a mika wa Bianca kofin ba tare da wata hamayya ba.

Serena wadda ta lashe manyan kofunan Tennis sau 72 a rayuwarta, a bana  ba ta lashe ko kofi daya ba saboda matsalar ciwon baya. Kuma ana ganin ba za ta sake yin wasa a bana ba saboda wannan matsala.

Bincike ya nuna Williams ta kamu da ciwon baya nebayan da ta haifi ’ya mace a shekarar 2017.

 

ADVERTISEMENT
Share