✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shagon Caka-Caka ya kashe Bahagon Garkuwan Ali-Fada a Legas

Shagon Caka-Caka daga bangaren Jamus ya kashe Bahagon Garkuwan Ali-Fada daga bangaren Guramada a damben da suka yi a filin wasan dambe na kasuwar Alaba…

 Wani sashe na ‘yan bangaren Jamus kenan. Shagon Caka-Caka daga bangaren Jamus ya kashe Bahagon Garkuwan Ali-Fada daga bangaren Guramada a damben da suka yi a filin wasan dambe na kasuwar Alaba Rago da ke Jihar Legas a yammacin Alhamis din da ta gabata.
Damben ya kayatar kwarai da gaske domin ya debi ’yan kallo masu yawan gaske wadanda suka hada da maza da mata.
A lokacin da suke damben, ’yan damben sun rika kai wa juna bugu da naushi inda a turmin farko aka kare ba tare da kisa ba.
Da aka dawo turmi na biyu Bahagon Garkuwan Ali-Fada ya rika kai wa Shagon Caka-Caka naushi babu kakautawa amma haka aka kare ba tare da kisa ba.
A turmi na uku Shagon Caka-Caka ya sauya dabara inda ya ki yarda ya hada jiki da Bahagon Ali-Fada ta haka ya rika kai masa naushi a ka da hakan ya sa wani lokaci sai Bahagon Ali-Fada ya taba kasa wanda alkalin wasa ya tabbatar da kisan Bahagon Ali-Fada.
Da Aminiya ta tuntubi  wanda ya yi kisan mai suna Shagon Caka-Caka ya bayyana farin cikinsa inda ya ce ya yi wa abokin karawarsa kisa biyu a dambe hudu da suka yi a wurare daban-daban a kasar nan.
Shi ma Bahagon Garkuwan Ali-Fada ya amince da kisan da Shagon Caka ya yi masa inda ya ce ya taba kashe shi a wani dambe da suka yi.
Shugaban gidan damben, Alhaji Aminu Kucere ya ce Shagon Caka-Caka ne ya yi kisa saboda hannayen Bahagon Garkuwan Ali-Fada sun taba kasa.
Ya ce,  “muna da ka’idoji a nan don kada a samu rikici. Idan aka yi dambe har hannuwan dan dambe suka taba kasa to an kashe shi. Dole dan dambe ya hakura.”