✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shaguna 60 sun kone a Kasuwar ’Yankatako da ke Kano

Wata gobara da ta tashi a Kasuwar ’Yankatako da ke unguwar Rijiyar Lemo a birnin Kano ta lakume dukiya mai tarin yawa. Wani ganau mai…

Wata gobara da ta tashi a Kasuwar ’Yankatako da ke unguwar Rijiyar Lemo a birnin Kano ta lakume dukiya mai tarin yawa.

Wani ganau mai suna Ibrahim Ado ya ce wutar ta tashi ne da misalin karfe 2:30 na dare.

Jami’in hulda da jama’a na  kasuwar, Shamsudeen Danwarure, ya ce gobarar ta lakume shaguna da dama da tarin katakon da ke jibge a kasuwar.

Jami’in hulda da jama’a na Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saidu Ibrahim, ya tabbatar da tashin gobarar yana cewa shaguna 40 tare da rumfunan je-ka-na-yi-ka (temporary) 20 sun kone kurmus.

Sai dai ya ce ba a kai ga gano musabbabin tashin wutar ba.