Da Dumi Dumi

Shahararren dan fim, Pran ya mutu a Indiya

Marigayi PranCikakken sunansa Pran Krishan Sikand amma an fi saninsa da sunan Pran. Ya dade cikin harkar fim a Indiya, wanda ya kasance cikin fim tun daga shekarun 1960. A Juma’ar da ta gabata ne ya mutu, a sakamakon jinyar da ya dade yana yi. Ya mutu ne yana dan shekara 93 a duniya.
Pran, wanda a baya ya kware wajen fitowa a bangarorin fim daban-daban, ya mutu ne a asibitin Lilabati da ke birnin Mumbai, inda nan aka yi jinyarsa. “Ya mutu ne daidai misalin karfe 8:30 na dare.” Inji dansa Sunil.
Tun da farko, an kwantar da Pran ne a asibiti, bayan ya yi korafin yana jin wahala wajen numfashi a ranar 30 ga watan jiya. Likitocinsa sun bayyana a lokacin cewa yana dauke da cututtuka daban-daban da suka hada da nemoniya da ciwon koda da sauransu. Ta kai ga sai da aka sanya shi ga injin taimaka masa wajen numfashi.
A lokacin kuruciyarsa, an san Pran sosai wajen kokari a fina-finai, musamman ya yi fice a fina-finan ‘Zanjeer’ da ‘Don’ da ‘Amar Akbar Anthony’ da sauransu da dama.
Pran, wanda ya saba fitowa a matsayin mamugunci a fina-finan, kamar kuma yadda yake fitowa a matsayin dan sanda ko uba, ya taba samun lambar yabo mai girma mai taken ‘Dada Sahen Phalke Award.’
An haife shi ne a ranar 12 ga Fabrairu, 1920 a birnin Delhi. Ya yi karatu garuruwan Kapurthala da Unnao da Meerut da Dehradun da Rampur, kasancewar mahaifinsa Lala Kewal Krishnan Sikand ya yi aikin gwamnati a wadannan garuruwa.
Tun da farko, Pran ya so ya zama mai sana’ar daukar hoto, amma kaddara ta canja masa kuduri, inda ya hadu da wani mai shirya fina-finai, wanda ya sanya shi cikin fim dinsa mai suna ‘Yamla Jat’ a 1940. Wannan fim ne ya fara fitowa a cikinsa kuma tun daga nan ya ci gaba. Daga nan ne ya fito a fina-finai kamar ‘Chaudhary’ (1941) da ‘Khandan’ (1942) da ‘Kaise Kahun’ (1945) da ‘Badnami’ (1946).

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya