✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shaidanu ke ruruta sabani a tsakanina da Obaseki – Oshiomhole

Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa Kwamared Adams Oshiomhole ya ce sabanin da ake samu a tsakaninsa da Gwamna Godwin Obaseki wadansu shaidanun mutane ne, suke…

Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa Kwamared Adams Oshiomhole ya ce sabanin da ake samu a tsakaninsa da Gwamna Godwin Obaseki wadansu shaidanun mutane ne, suke kawo shi domin biyan bukatar kansu.

Mista Oshiomhole ya bayyana haka ne a ranar Litinin da ta gabata, lokacin da yake karbar Gwamna Obaseki da ayarinsa da suka kai masa Gaisuwar Sallah a gidansa.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan ganawa ta sirri da suka yi a tsakaninsu, Oshiomhole ya ce “Wannan ganawar kamar kowace take, kuma a kullum muna tattaunawa da shi Obaseki” wanda ya bayyana shi a matsayin dan uwa  gare shi, ya ce wannan ziyara ta ba mu damar ganawa da juna da kuma sauran jama’ar da ya yi aiki da su a da. Ya ce abin takaici ne yadda kafofin watsa labarai ke haddasa rashin fahimta a kan wannan lamari da ya faru a Jihar Edo.

A jawabin Gwamna Obaseki ya ce kai ziyara ga wanda ya gada ba yau aka fara ta ba, kuma ya yanke shawarar yin Bikin Sallah ne tare da tsohon maigidansa. Ya ce wannan ziyara ta Sallah ce ga shugabannin Jihar Edo, kamar yadda ya kai wa tsohon Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa Cif John Odigie Oyegun da ya yi bikin cika shekara 80 a duniya. Gwamna Obaseki ya ce babu wani abu sabo a wannan ganawa, domin “Yau take Sallah dole mu yi biki tare, bai dade ba muka kammala bikin taya murna ga tsohon Shugaban Jam’iyyar APC a nan Benin, don haka na ga ya dace in zo kuma mu yi bikin Sallah da wanda ya gabace ni a mulki,” inji shi.

Sai Gwamnan ya ce masu tunanin akwai wata baraka a tsakaninsa da Oshiomhole sun yi kuskure babu komai a tsakaninsu, illa ci gaban Jihar Edo.