✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shamsiyya Isah: Ta fim zan zama makarin gubar da ke illata rayuwar aure

Shamsiyya Isah ta shigo fim da kafar dama, domin ba ta dade a harkar ba amma furodusosi suna rububinta , an alakanta jajircewarta wurin aiki…

Shamsiyya Isah ta shigo fim da kafar dama, domin ba ta dade a harkar ba amma furodusosi suna rububinta

, an alakanta jajircewarta wurin aiki ne ya kawo mata wannan farin jini, bugu da kari tana da saukin kai. A hirarta da wakilinmu ta yi bayanin abin da ya ja hankalinta har ta fara fim, inda kuma ta yi alwashin za ta zama makarin gubar da ke illata rayuwar aure. A sha karatu lafiya:

Za mu fara da jin takaitaccen tarihinki.
Assalamu alaikum masu karatu, sunana Shamsiyya Isah, an haife ni a Birnin Kano, amma na girma a Jihar Kebbi, kuma a garin Birnin Kebbi na yi karatun firamare da sakandare. Bayan na kammala sakandare kuma ban ci gaba ba sai na shiga harkar fim.
Me ya ja hankalinki kika shiga harkar fim?
Tun ina karama nake da sha’awar kallon fim din Hausa, ko aiki nake yi idan na ji an sanya fim din Hausa zan bari na je na kalla. Ko a makwabta na ji ana kallon fim din Hausa zan bazama na je kallo. ‘Yan fim din Hausa suna birge ni, zan iya cewa sha’awa ce ummul’aba’isin shiga ta fim.
Dalili na biyu da ya ja hankalina shi ne, na lura da yadda al’amuran aure suka tabarbare, kullum sai yawaitar mace-macen aure ake samu, haka ya jaza damuwa a gare ni sai na ga ta hanyar fim zan fadakar da jama’a har kwalliya ta biya kudin sabulu, na yi imanin zan iya zama makarin gubar da ke illata rayuwar aure.
Lokacin da aka fara dora miki kyamara a fim dinki na farko yaya kika ji?
Yawancin wadanda suka shigo harkar fim idan an fara dora musu kyamara jikinsu kan yi rawa; wadansu har da kyarma. A gaskiya ko lokacin da aka dora mini kyamara jikina ya yi rawa kamar ana yi mini kidan gangi. Na ji wani iri, na ji kamar ina cikin wata duniya.  Duk wanda ya kalli fim dina na farko zai ga ban saba ba, zai ga ina wani abu haka, wadda za a iya kirana da sabuwar shiga.
Da yaya kika shawo kan matsalar?
Ka san an ce yau da gobe ta wuce wasa, ana cikin daukar sai na ga kowa idan an zo nasa yana bakin kokarin ganin bai bayar da wata matsala ba. Sai na dauki hakan a matsayin kalubale a gare ni, na kuma sha alwashin tsayawa kai da fata gami da jajircewa wajen ganin an daina samun matsala daga bangarena. Na kuma dada kyautata mu’amalata da sauran ‘yan fim, inda wani darakta ya ce mini ba zan ci nasara ba sai na sake jikina kamar yadda kowa yake yi.
Ko akwai kalubalen da kike fuskanta?
A gaskiya babu wani kalubale da nake fuskanta. Daraktoci da furodusoshi da sauran ‘yan wasa sun dauke ni ‘yar uwa, sun ja ni a jiki; sun kuma ba ni dukkan kulawar da nake bukata; sun taimaka mini da kyawawan shawarwari, wadanda bayan na rika amfani da su sai na rika samun nasara.
Kin yi fina-finai kamar nawa?
Na yi fina-finai da yawa, don a yanzu ban san ko fina-finai nawa na yi ba, akwai ‘Basaja’ da ‘Alkuki’ da ‘Ra’ayi Zuci’ da sauransu.
Ko akwai wani burin da kike so ki cim ma a harkar fim?
Ba ni da wani buri face a ce fina-finan da na yi sun burge masu kallo, sun karu da darussan da za su fitar musu jaki daga cikin duma.  Burina a ce yau fim dina ya gyara zamantakewar rayuwar ma’aurata a gidajensu. Ya zamana fina-finaina sun zama waraka ga al’umma.
Sai na biyu, ina so na samu daukaka a harkar fim. Da fatan kuma Allah Ya daukaka dukkan ‘yan fim, hade da haskaka musu hanyar da za su zama wani tsani da jama’a su bi wurin samun mafita daga dukkan al’amuran da suka yi cacukwi da rayuwarsu.
Har zuwa yanzu akan yi wa ‘yan fim wani irin kallo, inda a wani wuri ake hantararsu, ko kin fuskanci hakan daga jama’a?
Alhamdu Lillahi, ban fuskanci irin wannan kallon ko hantara daga jama’a ba, amma a zahirin gaskiya mutane suna yi wa ‘yan fim kallon bata-gari wadanda ba su san ciwon kansu ba; jama’a na yi wa ’yan fim kallon wadanda ke lalata tarbiyyar jama’a maimakon gyara ta.  Wani abin da yake ba ni takaici shi ne, ka ji ana cewa duk wata ‘yar fim karuwa ce, ko kuma duk wani dan fim dan iska ne.  To ina so su sani ba haka ba, iskanci ko aikin kwarai na tare da mutum ne, shi ya sa ake cewa hali abokin tafiya. Idan da ma mutum dan iska ne a haka zai gudanar da rayuwarsa a kowace sana’a yake yi. Mutane su fahimci a kowace sana’a akwai bata-gari da kuma mutanen kirki. Kodayake an ce wake daya shi ke bata gari. A fahimta kowace sana’a mutum yake yi akwai hanyar zunubi da kuma lada, ya danganta da yadda mutum zai gudanar da sana’arsa ne, bari na ba ka misali, idan mutum likita ne, zai iya zabar hanyar kwarai wurin jinyar jama’a don su samu lafiya; ko kuma ya zabi hanyar banza kamar zubar da jiki, yin allurar hana haihuwa da sauransu. Haka idan mutum dan jarida ne zai iya watsa labarin karya ko wanda zai haifar da tashin hankali, kamar kuma yadda zai iya bayar da labaran da za su wayar da kan mutane. Don haka kada mutane su rika yi mana kudin goro, hakan ba adalci ba ne.
Ko kin fuskanci wata matsala daga iyaye kan harkar fim?
A gaskiya lokacin da na ce musu zan shiga fim ba su amince ba, inda ‘yan uwa da abokan arziki suka yi maganganu iri-iri har na ji kamar na hakura. Bayan al’amarin ya lafa ne sai na samu mahaifana na yi musu gamsasshen bayani, cikin ikon Allah suka fahimci alherin da ke cikin harkar fim; suka fahimci harkar fim ba harkar banza ba ce; suka kuma fahimci a kowace sana’a akwai hanyar wuta da aljanna.
Wane kira kike da shi ga masu kallo?
Babban kirana ga masu kallo shi ne, su daina yi mana kallon wasu bata-gari, idan suka ci gaba da yi mana irin wannan kallon sakon da muke son isar musu ba zai yi musu amfani ba. Yawancin mutane kuma sukan yi amfani da jita-jita ne wurin yi mana kallon bata-gari, don haka ina so su daina yin amfani  da abin da ba su gani ba, su sani kazantar da ba ka gani ba tsabta ce a tare da kai.  Ya kamata komai mutum zai yi ya rika bincike a kai.
Yaya batun aure?
Manzon Allah ya ce idan har mace ba ta gidan mijinta ya zamana tana cikin kabarinta, don haka hannuwana a bude suke don amsar aure idan har ya zo mini, amma a yanzu haka a kasuwa nake. Don haka fatana a yanzu shi ne, na gan ni a dakin mijina don na nemi aljannata, duk da cewar kowa ya san aure da mutuwa duka na Allah ne, idan suka zo babu makawa sai an yi. A sani da duk duniya za a taru don na yi aure, idan Allah bai yi ba babu yadda za a yi.
Wane irin launi kika fi so?
Na fi son shudi da kukunmadi da kuma ja.
Abinci fa?
Na fi son abincinmu na gargajiya, kamar tuwon shinkafa da miyar taushe, ko tuwon masara da miyar kuka da aka yi da kayan ciki, a sanya garin yaji da kuma man shanu. Sai dai wani lokaci nakan ci indomie da kwai da kuma chips, sannan ina son kayan makulashe (snacks) da cakulet da sauransu.

Kalankuwar fina-finai ta Cannes: Yadda karrama fim din badala ta haddasa tarzoma a Faransa

Labarai daga Bashir Yahuza Malumfashi (Da Rahoton Waje)

A Lahadin da ta gabata ce aka rufe kalankuwar fina-finai ta duniya mai taken ‘Cannes Film Festibal 2013’ wacce aka gudanar a kasar Faransa.
Kalankuwar, wacce ita ce karo ta 66 da aka gudanar, ta haifar da rudani, inda wani fim na badala ya samu babbar kyautar karramawa. A yayin rufewar ne aka zabi fim din ‘Blue is the Warmest Colour’ wanda wani mai bayar da umurni a fina-finai, dan kasar Tunisia, Abdellatif Kechiche ya shirya, aka yi masa karramawa ta musamman a matsayin fim din da ya yi fice daga fina-finan da aka gabatar.
Fim din, wanda Adele Edarchopoulos da Lea Seydoud ke jagorantar sauran ’yan wasa a cikinsa, an shirya shi ne daga labarin soyayya, kamar yadda yake a littafin Julie Maroh.
Fim din na dauke da labarin wata budurwa ce da ta kamu da son wata mata, wacce ta dan grime ta kadan. Yana bayyana yadda soyayyar mace da mace ke kasancewa, wadda haka ta haifar musu da la’antattar dabi’ar nan ta madigo.
Ba a jima da bayyana zaben wannan fim a matsayin gwarzo ba, sai al’ummar Faransa, musamman masu ra’ayin ’yan mazan jiya suka kwarara a titunan birnin Paris suna zanga-zangar nuna adawa da la’antar wannan hukunci. Haka kuma, dama tun farko a makon jiya ne aka zartar da dokar da ke ba al’ummar Faransa ’yancin auren jinsi daya. Dalili ke nan masu adawa da wannan doka suka alakanta karrama wannan fim da ita dokar, wanda haka ya sanya suka nuna bacin ransu. An samu bayanin cewa sama da mutum 150, 000 suka shiga cikin wannan zanga-zanga.
Baya ga fim din na badala, sauran wadanda suka samu kyautar karramawa a kalankuwar ta Cannes sun hada da fim din ‘Inside Llewyn Dabis’ wanda ’yan uwa Coen Brothers suka bayar da umurninsa. Haka kuma fim din ‘Like Father, Like Son’ na darakta Hirokazu Kore-Eda, dan kasar Japan ya samu kyauta. Haka shi ma fim din ‘Heli’ na dan kasar Medico, Amat Escalante, ya samu kyautar gwarzon darakta.

Mawakiya Weird MC ta kama hanyar amarci?
Mawakiyar nan da sunanta ke kada tambura a Kudancin Najeriya, Weird MC ta mike wurjanjan domin fuskantar sabon faifan wakokinta, inda wasu ma suka fara karar da cewa ta fara shirye-shiryen aurenta.
Mawakiyar wadda a makon da ya gabata aka ganta tana ta fafutukar gudanar da ayyukan fitar da sabon faifanta da kuma tallafa wa sabon mawaki, Shuley Dee, ba ta gajiya ba. Baya ga wannana, an ga yadda take ta shirya wasanni a manyan biranen Kudancin Najeriya.
A cikin irin wadannan wasanni nata, ta yi wasa da kungiyar mawaka ‘Salt-N-Pepa’ inda a nan ne ta rera fitattar wakarta ta “Ijoya” da sabon salo, sannan kuma ta hada da wakar “Fiesta.”
A yayin da Weird take ta wannan fadi-tashi a sana’arta, labari kuma tuni ya bazu cewa tana ta shirye-shiryen ganin ta zama amarya, nan ba da dadewa ba. Da aka tambaye ta game da wannan batu na aure, ganin cewa ta dade babu miji, sai ta wayance, ta ki bayyana ainahin labarin da ke ta cika gari, cewa ta kusa yin aure. A nata batun game da aure, cewa ta yi: “A’a, a’a, wannan batu sam ba ya cikin ’yan kayana, domin kuwa ba ni da lokacinsa yanzu. A yanzu babu abin da na tunkara sai batun fitar da sabon faifaina, don haka batun aure ba yanzu ba.”

Ranar da mawaki Tuface ya kusa halaka a jirgi
A Lahadin da ta gabata ne wani hatsarin jirgin sama ya kusa ritsawa da mawakin nan da ya dade yana fantamawa a duniyar mawakan kasar nan.
Mawakin, Tuface Idibia, ya shigo jirgi ne daga kasar Afrika Ta Kudu zai zo Legas. Yana cikin jirgi da tawagarsa, yana ta sauraren waka daga na’urarsa sai ya fara jin kaurin waya na konewa. Lamarin ya kara ta’azzara, inda wutar jirgin gaba daya ta dauke. Nan take kuma fasinjoji suka fara karaji, wasu na cewa: “Jirgin nan zai tarwatse!”
Inda abin ya zo da sauki shi ne, lokacin da matukin jirgin ya bayyana cewa lallai jirgin ya samu matsala a bangaren lantarki, don haka fasinjoji su natsu, jirgin zai yi saukar gaggawa. Daga nan ne ya juya akalar jirgin suka koma kasar Afrika Ta Kudu.
Daga nan ne shi kuma Tuface ya yi ta lallashin tawagarsa, yana shawartarsu da cewa kada su razana. Suna isa filin jirgin sai suka yi sa’a kafafun jirgin suka bude, wanda haka ya ba su damar saukowa lafiya. Nan da nan kuwa aka dauke fasijojin, aka canja musu wani jirgin.