✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shanu sun cinye gonakin shinkafa sama da 80 a Jihar Taraba

Garken shanu masu yawan gaske sun cinye gonakin shinkafa sama da Tamanin a yakin Yelwa da Dubeli a kananan hukumomin Lau da Arbo- Kola a…

Garken shanu masu yawan gaske sun cinye gonakin shinkafa sama da Tamanin a yakin Yelwa da Dubeli a kananan hukumomin Lau da Arbo- Kola a Jihar Taraba adadin  asaran da manoman shinkafa suka yi a sanadiyyar barnar da shanu suka yi, ya zarce Naira miliyan 74.

Wakilinm da ya ziyarci yankin wanda ke da nisan sama da kilo mita arba’in daga garin Jalingo babban birnin Jihar kuma wanda ke cikin kungurmin daji ihun ka banza ya iske gonakin shinkafa  masu yawan wabanda shanu suka cinye baki baya.

Gonakin wabanda suke cikin babban tafki kusa da kogin Benuwai ya kasan ce inda jama’a daga sassan jihar har ma da wasu jihohi ke gudanar da noman shinkafa a lokutan damina da rani.

Baya daga cikin gonakin da shanu suka cinye  mallakar wani manomi ne mai suna Dokta Kabiru  Abiso daga Jihar Barno. Yayin da ita wannan Gonar manajanta, mai suna Sani Shugaba ya bayyana cewa an shuka irn shinkafa sama da buhu ashirin da biyar  a cikinta.

Manajan ya bayyana cewa an  karbi hayar gonar a wajen Dakacin garin  Dubeli akan kubi naira dubu bari hudu da hamsin.

Ya ce sun bauki lebururi  sama da mutum  bari tara. Sani shugaba ya kara da cewa, mai gona ya karbi bashi daga babban bankin Najeriya watau (CBN) na aikin noman Shinkafa.

Sani shugaba ya bayyana cewa shinkafan su ta nuna kuma ya rage kwanaki goma su fara yanka makiyayan suka sanya shanunsu suka cinye gonar. Ya ce su na saran cewa, wasu sun sami sama da buhu dubu ashirin da biyar a gonar amma ko kwano baya wasu basu samu ba.

Wani manomi mai suna Aliyu Hassan ya shaidawa wakilinmu cewa, ya shuka buhu ashirin da biyar a gonarsa amma shanu sun cinye gonar kwana goma kacal ya fara yankan shinkafarsa.

Aliyu Hassan ya ce, ya sayar da taraktarsa da mota Hilub duk ya sanya a gonarsa amma yanzu ya koma hannu ba bu.

Ya ce, ya sa  ran cewa zai samu buhu bari biyu da arba’in, ya kara da cewa, sama da manoma tamanin a yankin makiyaya suka cinye wa gonaki .

Shi ma wani manomi mai suna Zakari Usman ya ce, makiyayan sun cinye masa gonar shinkafar baki baya.

Ya ce, za a sami karancin shinkafa a kasuwannin jihar domin yankin na Yelwa na gaba wajen samar da shinkafa a jihar Taraba kuma gashi makiyaya sun cinye mafi yawan gonakin shinkafa a yankin.

Zakari Usman ya ce, akwai manoma masu noma buhu dubu baya da fiye da haka amma duk shanu sun cinye.

Zakari Usman ya ce akwai bukatar gwamnatin jihar Taraba ta sanya solar domin hana makiyaya barna a gonakin jama’a.