Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Sharbar dankali

Kayan hadi:

* Kayan ciki

ADVERTISEMENT

*Dankalin Turawa

* Kayan kanshi

ADVERTISEMENT

* Sinadarin dandano

*Kayan miya

* Ganyen fasili

 

Yadda ake yi:

Da farko, uwargida za ki samu kayan ciki na rago ko tunkiya, sai ki wanke shi tas. Ki fitar da duk daudar da ke makalewa, sai ki yanka su kanana, sannan ki dora a wuta ki zuba kayan kanshi da sinadarin dandano da gishiri a zuba albasa da tafarnuwa mai yawa. Sai ki bar shi ya dahu. Sannan ki fere dankali ki yanka shi kanana a kwance. Idan kin tabbatar kayan cikin sun dahu, sai ki dauko jajjagen kayan miya ki zuba a ciki, tare da man girki. Idan ya yi kamar minti biyar, sai ki zuba  dankalin nan da kika yanka a ciki.

Sai ki zuba sinadarin dandano a ciki ki juya. Ki bar shi ya dahu. Amma fa shi wannan girkin ruwa-ruwa ake cin sa.

Don haka, idan ana dahuwa za a tafasa ruwa, a ajiye a gefe ko akwai bukatar karawa. Idan ya dahu sai a sauke, a ci shi da ruwa-ruwa.