Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Sharhi da tsakure daga littafin Kundin Hirarrakin Bukar Usman (2)

Marubucin littafin Kundin Hirarrakin Bukar Usman, Khalid Imam ne a tsakiya, tare da editocin jaridun Daily Trust (Saturday) da Aminiya, yayin da ya ziyarce su a makon jiya
Marubucin littafin Kundin Hirarrakin Bukar Usman, Khalid Imam ne a tsakiya, tare da editocin jaridun Daily Trust (Saturday) da Aminiya, yayin da ya ziyarce su a makon jiya

Sunan Littafi:                        Kundin Hirarrakin Bukar Usman

Sunan Marubuci:                 Khalid Imam

ADVERTISEMENT

Kamfanin Wallafa:              Whetstone Arts, Kano

Shekarar Wallafa:               2018

ADVERTISEMENT

Yawan Shafuka:                   366

 

Kamar yadda muka faro sharhin littafin nan a makon jiya, mun tsunduma ne wajen tsinto wasu muhimman sassa da kalamai a cikin littafin, wadanda za su kara mana fahimtar kunshiyarsa. Bisa ga wannan, Dokta Bukar Usman ya kasance dan kabilar Babur, amma abin mamaki, baya ga Ingilishi babu wani harshe da yake rubutu da shi illa Hausa. Irin hidimar da yake wa adabin Hausa, abin ya gawurta. An tambaye shi dalilin da ya sanya yake wannan aiki da hidima ga harshen Hausa, sai ya ba da amsa a shafi na 56 cewa:

“Kamar yadda ka ce Allah ne Ya ba ni fasahar yin Hausa ko na yi rubutu da Hausa, kuma na gaya maka ni ba Bahaushe ba ne, amma na soma karatun boko da Hausa, irin littattafan su Alhaji Abubakar Imam, Mu Kara Karatu, irin su Ruwan Bagaja da sauransu duk a lokacin na karanta su. Tun daga lokacin abin ya daukar min hankali har na fara tunanin littattafan Hausa, saboda irin wadannan littattafan ana karancinsu da yawa. Na ce ni ma bari in duba ko zan iya rubuta wani abu da Hausar Babur, amma zan ba wa mutane wadanda za su iya dubawa su ga dai ba irin Hausar da kamar shi Alhaji Ibrahim Biu Kakaki ya gaya wa Sardauna lokacin da aka ba shi Minista ba ce, ya ce “Ranka ya dade Allah Ya sa ka gaji ubanka.” Ka ga wannan Hausar ai ba daidai ba ce. Sai Sardauna ya ce “A’a ga shi na ba ka mukami kana zagina (raha).” Ta haka ya sa na kara tunanin rubuta wani abu na bai wa mutane wadanda suke jin Hausa domin sun san Hausar zamani, wanda za ta sa irin kura-kuran da Kakaki ya yi a gaban Sardauna wadansu masu zuwa ba za su yi irinta ba.”

Wani abin mamaki kuma, kusan dukan littattafan da Bukar ke rubutawa, kyauta yake raba su ga al’umma, a shafi na 59 an tambaye shi cewa: To wannan rubutu ka yi shi ne don riba ko domin ka taimaka wa yara, ko kuma duka biyun? Sai ya amsa da cewa: “Idan riba ta zo mutum zai so, tunda na riga na yi ritaya, amma ba shi ne dalilin da ya sanya na yi ba, don a yanzu haka farashin da za mu saka ba zai ishe mu ko biyan kudin bugawa ba.”

A game da gidauniyarsa ta tallafa wa al’umma, ya amsa tambaya dangane da haka a shafi na 64, inda yake cewa: “Lokaci ya yi da ya kamata a ce mun fuskanci  cewa ba komai gwamnati za ta iya yi wa jama’a ba. Dole ne mutane daidaiku da kungiyoyi su tashi haikan wajen ganin an samar da wani nau’i na taimakon juna. Hakan na ga ya dace mu kafa wannan cibiyar. Wannan cibiyar a yanzu haka tana da mambobi guda saba’in da kuma kwamitin amintattu mutum goma.”

Game da kalubalen da mutum kan fuskanta a rayuwar aiki ko sana’a kuwa, akwai abin koyi a rayuwar Dokta Bukar. A shafi na 66, ya amsa tambayar da ke cewa, Kasancewar ka gogu sosai a fannin aikin gwamnati, masu karatu za su so jin irin kalubale da fadi-tashin da ka fuskanta a aikinka kafin ka yi ritaya. Shi kuwa ya amsa da cewa:

“A cikin aikin gwamnati, a lokacin da mutum yake aiki a kasa irin Najeriya, wacce tana daya daga cikin kasashen da ake kira da masu tasowa, akwai abubuwa da yawa, wadanda ba sa tafiya daidai. Na daya, koda yake mutane na neman a gyara musu al’amuran zamansu na duniya, akwai batun kudi, akwai kuma batun tashin hankali, ko ta wajen addini, ko ta wajen fadan mutane saboda bambancin kabila ko bangaranci da fada domin neman wurin zama ko na noma. A aikin da nake yi na bangaren sashina, irin wadannan abubuwa suna faruwa sosai. Matukar mutum yana aikin gwamnati irin sashin da nake, dole ne abubuwa irin haka su dame shi. Amma dai na yi aikina tukuru, na kammala lafiya. Kuma kafin in bari sai da na kai mukamin Babban Sakatare a Ofishin Shugaban Kasa. Tunda na kammala lafiya, ya zama dole in yi godiya ga Allah, in ce alhamdu lillahi.”

Ga mutumin da ya rayu a duniya, ya aiwatar da aiki ko sana’a tare da cudanya da mutane mabambanta a cikin shekaru masu yawa, yana da muhimmanci ya rubuta abin da ya sani domin ’yan baya su dauki darasi. Domin jaddada muhimmancin rubutu, musamman na tarihin mutum, ga abin da Dokta Bukar yake cewa a shafi na 70:

“Kamar misalin littafin da na rubuta na tarihin kaina, na rubuta shi ne saboda a cikin rayuwata, abubuwa da yawa sun faruwa ga mutum, wasu na farin cikin wasu kuma na bakin ciki, dalili ke nan da ya sa na rubuta, domin mutane su karu da darussan rayuwa, musamman ta wajen da na yi abin kirki. Sannan kuma su kare kansu daga fadawa cikin irin kura-kuran da na yi a rayuwa. Haka ma littafin da na rubuta game da aikin gwamnati, ina son wadanda ke bayanmu su karanta domin su kwaikwaya. Ka san harkar tafiyar da gwamnati abu ne mai wuya, don haka ina ganin ya dace a ba wa matasa dama su ma su dana. Ba kamar yadda wadansu suke yi ba, bayan sun yi aiki shekara talatin da wani abu, amma har yanzu suna so su koma.”

A lokacin da garkuwa da mutane don amsar kudin fansa ta kankama a Najeriya, an tambayi Dokta Bukar cewa bisa gogewarsa a matsayinsa na wanda ya taba zama Babban Sakataren Ayyuka Na Musamman, ko zai goyi bayan samar da doka kan yin garkuwa da mutane (kidnapping) da ya zama ruwan dare? Shi kuwa a shafi na 89 sai ya ce:

“Wajibi ne a rika samar da dokoki domin a tafiyar da al’umma cikin tsari. Bayan kasarmu ta fito daga Yakin Basasa sai kuma ta fuskanci matsalar fashi da makami. Daga lokaci zuwa lokaci mukan yi dokoki a kan fashi da makami. Garkuwa da mutane sabon al’amari ne, amma na yarda da wadanda ke cewa shi ma zai wuce. Ina jin Shugaban Ma’aikata na yanzu ya ce jami’an tsaro za su fito da sababbin hanyoyi na fuskantar laifuffuka kasancewar suna zuwa ta hanyoyi daban-daban. Abin yana da cutarwa kuma yana kara yaduwa. Muna bukatar mu kawar da shi. Suna amfani da wayar tafi-da-gidanka wajen shirya abin da za su aikata. Wannan ma kalubale ne. Ina fatan za a rika zakulo wadanda ke amfani da wayar tafi-da-gidanka suna neman kudi. A halin da muke cikin yanzu, kamfanonin wadannan wayoyi suna taimaka wa jami’an tsaro. Amma na yi imanin za a magance matsalar saboda kowace cuta tana da magani, yin dokoki ga irin wannan matsala yana daga cikin hanyoyin samar da waraka. Za mu iya dakushe karfinsa, sannan jami’an tsaro su yi kokarin gano cewa ko hanyoyin da suka samar za su iya taka wa masu yin garkuwar birki.”

Ga duk kasar da ke son ci gaba, ya zama wajibi al’ummarta su mai da hankali wajen karatu da rubutu, a shafi na 95, an tambayi Dokta Bukar cewa, ko akwai wani kira da zai yi a matsayinsa na marubuci dangane da karatu da rubutu a cikin al’umma. Ya ce:

“Haka kuma cikin abubuwan da ke haifar da karancin karatu, akwai talauci kuma akwai jahilci. Ta fannin talauci, shekaru da yawa da suka gabata har zuwa yau, mutane na kuka da rashin abin hannu, wato suna kuka da talauci da ya yi yawa cikin al’umma. Kamar misalin yau da muka halarci taron gabatar da wani littafi na ‘Almajiri’ ka ji dai irin abubuwan da aka tattauna a wurin. Ka ji yadda ake cewa mutane na kallon wadanda ba su yi karatun zamani ba a matsayin jahilai, ko da kuwa sun yi karatun allo, ganin cewa tunda ba su iya karatun boko ba, wanda kuma ba haka abin yake ba.”

Harshen Hausa ya yi karfi tare da tasiri kusan a ce duk duniya. Dokta Bukar ya bayyana haka a shafi na 100, inda yake bayyana dalilin da ya sanya ya zabi harshen a matsayin hanyar aika sako ta hanyar rubutu. Ga abin da yake cewa: “Na zabi rubutu da harshen Hausa ne saboda ina son sakona ya isa ga mutane da yawa, kuma su ne mutanen da suke kaunarmu. A kasa irin Najeriya wadda take tinkaho da cewa tana da kabilu dari biyu da hamsin, amma abin takaici harsuna suna mutuwa kuma akwai hasashen cewa akwai yiwuwar samun bacewar harsuna a Najeriya a shekaru masu zuwa. Misali, lokacin da Turawa suka shiga Austireliya, kasar na da harsuna dari biyu, amma a yau da wahala idan sun kai ashirin. Yanzu suna nan suna ta kokarin farfado da harsunan da suka mutu tare da ci gaba da koyar da su.”

Daya daga cikin darussan littafin nan shi ne, kira tare da jawo hankalin al’umma su daraja al’adunsu. An tambaye shi a shafi na 107 na littafin nan cewa, yana jin cewa har yanzu tatsuniyoyi suna da muhimmanci ga al’ummarmu a yau? Ga amsar da ya bayar:

“A mahangata, idan mutum ya yi karatu, ya yi ne sakamakon wani abu da yake nema. Idan ka yi haka can kasa sosai, za ka tarar da arziki jibge. Ko man fetur din nan da muke da shi, ba sai da muka yi haka can kasa aka same shi ba? A baya na fada cewa mutum ya dauka ya shiga harkar tatsuniya ce domin ya tono abin da na bayanmu suka binne; kada mu taba zaton cewa iyayenmu da kakanninmu jahilai ne. Gaskiya ce hanyar da suka bayar da ilimi ta gargajiya ce, amma wannan al’adar ta a fada da baki, a fahimtarmu tana dauke da sakonni masu tarin yawa.”

Domin kara jaddada muhimmancin karatun littattafan hikaya kuwa, ga abin da Dokta ya ce a shafi na 112: “Har ila yau mun karanta wasu labarun da shahararrun marubuta irin su Dokta Abubakar Imam suka rubuta a lokacin. Kamar wani labari da wani ya ce ya gaji da zaman duniya saboda talauci, shi a kashe shi. Ya je wajen sarki ya ce yana so a kashe shi, ya gaji da zaman duniya, aka kai shi fili za a kashe. Sai wani daga cikin ’yan kallo ya ce don Allah idan an kashe shi yana son bantensa. Nan da nan mutumin ya ce ranka ya dade ku dakata, a mayar da ni wurin sarki! Aka mayar da shi, sai ya ce ashe a cikin duniyar nan akwai wanda na fi dukiya?”

Shin wadanne irin mutane ne ya kamata a yi mu’amala da su? Dokta ya bayyana irin zabinsa a shafi na 154 zuwa 155, inda yake cewa: “Ni fatana shi ne wadanda zan yi mu’amala da su, su kasance mutane nagari da za su ce Allah Sarki mun tuna wane saboda kaza da kaza, fiye da son a tuna da ni saboda wani abu. A irin wannan fadi-tashin za ka hadu da mutane wadanda saboda shakuwa za su yi kukan rashinka yayin da Allah Ya yi maka rasuwa. Mutum ba ya sanin muhimmancin abu sai ya rasa shi. Don haka makusanta da wadanda aka yi gogayyar rayuwa tare ne za su fadi abin da za a iya tuna mutum da shi, amma kash, lokacin mutum ba ya nan ballantana ya sani.”

 

Za mu kammala makon gobe in sha Allahu