✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sharhin Littafi: Tarkon Mutu’a ko Tarkon Shaidan?

Sunan Littafi:                       Tarkon Mut’a (Wasan Kwaikwayo) Sunan Marubuci:                Bashir Yahuza Malumfashi Shekarar Wallafa:              2019 Kamfanin Wallafa:             Gizago Publishing Enterprises Yawan Shafuka:…

Sunan Littafi:                       Tarkon Mut’a (Wasan Kwaikwayo)

Sunan Marubuci:                Bashir Yahuza Malumfashi

Shekarar Wallafa:              2019

Kamfanin Wallafa:             Gizago Publishing Enterprises

Yawan Shafuka:                  100

Lambar ISBN:                       978-2149-99-3

Farashi:                                 Naira 500

 

Amfanin rubutu a cikin al’umma shi ne domin a fadakar, a ilimantar, a kuma nishadantar da kuma yin hannunka mai sanda ko fargar da mutane a kan wani abu da ya gallabi al’umma; domin a kawo gyara ko a bari gaba daya.

Wannan littafi wanda Malam Bashir Yahuza ya rubuta a farkon shekarar nan ta 2019, wanda Kamfanin Gizago Enterprises da ke Abuja ya wallafa, ya zo da wani babban al’amari wanda aka dade ana yin tsokaci a kansa; wato shi ne “Auren Mutu’a” wanda wani sashe na Musulmi mabiya Shi’a ke aiwatar da shi.

Shi wannan littafi da nake yi wa sharhi a yau, an shirya shi ne a tsarin wasan kwaikwayo, inda aka shirya shi sannan aka dora shi bisa bagiren sakamakon binciken da wani Malamin Musulunci mabiyin Sunnah, Farfesa Umar Labdo na Jami’ar North-West da ke Kano ya gudanar a kan Shi’a da akidojinta.

Littafin na Tarkon Mutu’a yana da yawan shafuka 100 daidai, shafuka 9 na gabatarwa da shafuka 91 na gundarin littafin. Haka  marubucin ya yi amfani da sassaukar Hausa wajen rubuta shi, sannan an yi wa littafin aiki mai kyau da inganci. An yi amfani da ka’idojin rubutu sosai.

Wani abin burgewa da littafin shi ne, tun daga gabatarwarsa aka yi iya kokari wajen bayyana ma’anar Auren Mutu’a. Kamar yadda mai gabatarwar ya bayyana: “Shi dai Auren Mutu’a shi ne auren wucin-gadi ko kuma a ce auren da ba na dindindin ba, ko a ce auren kwana daya ko biyu ko kuma auren yarjejeniya, ko kuma auren kowa ya kama gabansa bayan gama mu’amalar.”

Har ila yau, a cikin gabatarwar an tabbatar da cewa a farkon Musulunci an yi wannan aure, amma daga baya aka haramta shi bisa ga ruwayar Ali bn Abu Dalib (RA), cewa Manzon Allah (SAW) ya hana Auren Mutu’a da cin naman jaki a lokacin Yakin Khaibar.

A iya nazarin da aka yi, Auren Mutu’a hanya ce ta yada fasadi da alfasha da barna a cikin al’ummar Annabi Muhammad (SAW) kuma hakan ya kara bayyana a ire-iren rubuce-rubucen da aka yi a kan  Shi’a, musamman baya ga kuma littattafansu kamar irin su ‘Man la Yahdarruhul Fikih.’

A iya cewa wannan littafi na Auren Mutu’a ya zo a daidai lokaci, idan aka yi la’akari da halin da Musulmi a Najeriya da sauran kasashen duniya ke fama da rabuwar kawuna, rudu da kuma shigowar bakin bidi’o’i da suka baibaye addinin Musulunci, suka kuma yi tarnaki ga ci gaban Musulmi da Musulunci.

Shi dai littafin Tarkon Mutu’a yana ba da labarin wata yarinya ce wadda ta gama Kwalejin Kimiyya da Kere-Kere ta Hassan Usman Katsina, wadda kuma ’ya ce ga Malam Bello, wadda wani saurayi mai suna Dandangi ya yaudara suka yi Auren Mutu’a. Wannan aure ne kuma ya kai ta ga daukar ciki ba tare da iyayenta sun sani ba, inda bayan cikin ya bayyana a gare ta suka yi kokarin zubar da shi a wani kemis a Katsina. Zuwansu wannan kemis ne sai suka tarar da rikici mai firgitarwa, inda aka zubar wa wata ciki ta mutu, matasa suka zo neman mai kemis din. Kasancewar ba su tarar da shi ba, sakamakon hargitsin wurin ya sa Nana ta fadi a daben kwalta, cikin da take dauke da shi ya zube. Shi kuma Dandangi mota ta buge shi ya rasa kafafuwansa. Nana ta koma gidansu ta nemi yafiyar iyayenta a kan abin da ta aikata.

Lallai Auren Mutu’a masifa ne, domin bai da bambanci da dadiro, tunda ba shaidu, babu waliyyai kuma babu siga, wanda haka ya yi hannun riga da Sunnar Ma’aiki (SAW), Allah Ka yi mana tsari  da shi.

Kuma kalubale ne a kan Musulmi a kara  neman ilimi domin jahilci ne jagorar aikata duk wata ta’asa ko shaidanci.

Babu shakka littafin nan kundi ne mai cike da fadakarwa, ilimantarwa da kuma nisahadantarwa. Ya kamata a tanadar da shi ga dakunan karatu da majalisun karantarwa na mata da maza, domin kuwa zai amfanar da daliban ilimi da kowa da kowa.

Malam Aminu marubuci ne kuma mamba a Kungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA) a Jihar Katsina (08065032730).