Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Sharhin Wakar Bauna ta Malam Maharazu a shekarar 1944

Sharhin Wakar Bauna ta Malam Maharazu a shekarar 1944
Sharhin Wakar Bauna ta Malam Maharazu a shekarar 1944

Taskar tarihi a yau na dauke da tarihin da ke cikin “Wakar bauna” wadda Malam Maharazu Barmu Kwasare ya rubuta tun shekarar 1944 miladiyya wadda ta yi daidai da shekarar 1365 bayan hjirar Manzon Allah (SAW). Malam Maharazu ya rubuta wakar yana da shekara 28 da haihuwa kuma, al’amarin baunar ya faru cikin wannan shekarar kamar yadda Maharazu ya ambata”

Daga Dano Balarabe Bunza

ADVERTISEMENT

 

Bana an sha wuya an sha takima,

ADVERTISEMENT

Sanadin kaddara an tar da bauna.

 

Bauna dabbar daji ce mai kamanni iri daya da saniya. Wannan ne ya sanya Hausawa ke yi mata kirari da cewa, “Bauna saniyar sake, amma ba dukiyar uban kowa ba”. Bayan haka , abincin da saaniya ke ci shi ne abincinta kamar dawa da harawar wake da sauran ciyayi. Ga abin da Malam Maharazu ya fada dangane da abincinta cikin wani baiti kamar haka:

 

Da dawowi da wakaikan harawa,

Abincin nagge shi taka dora tamna.

 

Bauana dabba ce mai tsananin karfi da rashin tsoro ko saunar abubuwa kuma, tana cutar da mutane kwarai da gaske musamman idan aka yi la’akari da abin da Malam Maharazu Kwasare ya ce, kamar haka:

 

Kashewa dai takai ba ci takai ba,

Akwai cuta, akwai sabai ga bauna.

 

Idan ta gani ita ba dubara,

Saurin zaburam ma mutum ga bauna.

 

Mahalba masu ba-duhu mau tsafi,

Su ka shiga duhu su kashikke bauna.

 

Au ko jan Bature shi da soja,

Su ka shiri su zo su kashikke bauna.

 

Ya wuce nagge karfi ya fi doki,

Kutunkun auru bas hi kama da kinna.

 

Baunan namiji ne kamar yadda aka sami labari ga wadanda suka sami ganin shi, da kuma abin da Malam Maharazu ya fada a cikin  wasu baitocin wakarsa kamar haka:

 

Namiji fan a mutane sunka gane,

Halan matarsa tat tafi yamma bauna?

 

Da lawayensa gas u suna ta shillo,

Nan aka san kutunkun sauru bauna.

 

Baunan ya fito sanadiyar bacewar matarsa ko kasheta da aka yi duk da yake tana mutuwa ko ba saboda wadannan dalilai da aka ambata ba. Malam Maharazu ya fadi cewa. Ya rubuta wakar saboda labarin da aka ba shi na baunar inda ya ce:

 

Ga farkon jin mu gun Nakki na lambu,

Uwa da diya suna ban ruwa ga guna.

 

Da farko baunan ya bayyana a wasu garuruwa ba tare da hallaka kowa ba. Wannan ya faru saboda rashin tsangwamar sa da ba a yi ba. Da ya kai wasu wuraren da aka kula masa tare da tsangwama, sai ya fara bayyana halinsa na dabba ya ci gaba da halaka jama’a. Abin da ke tabbatar da Baunan ya bi wasu garuruwa ba tare da illanta kowa ba shi ne abin da Maharazu Barmu ya fada kamar haka:

 

Gidan Aiki da Maudawa da Lemi,

Da Rumbuki duk batun da sukai na bauna.

 

Da Jangebe Tudu da Gidan Makera,

Da Gulbi duk batun da sukai na bauna.

 

Da Kandam har gidan Inda da Gelgel,

Da Alkammu duk batun da akai na bauna.

 

Wuce garuruwan ke da wuya ga bauna sai halinsa ya motsa na rashin hankalin dabba kuma, ko babu komai an bayyana cewa dabba ce marar hankali da ba ya amince wa kowa kusa gare shi. Baunan ya fara cutar da mutane  inda ya fara ganin wata mace da diyarta suna ban ruwa a guna cikin daji. Diyar ta fara ganin baunar sai ta gaya wa uwarta cewa ga kura nan domin bata san bauna ba. Da baunan ya gan su sai ya zaburo zuwa gare su. Da isarsa gare su sai ya banke su ya wuce zuwa gaba ba tare da komowa kansu ba. Ga abin da Malam Maharazu ya ce:

 

Ga farkon jimmu gun Nakki na lambu,

Uwa da diya suna ban ruwa ga guna.

 

diya tat tashi tac ce inna kura,

Da tatc tcinki su ba fashi ga bauna.

 

Sai taz zaburo duk tak kide su,

Tay yo yamma nan aka gane bauna.

 

Da baunan ya wuce uwar da diyarta sai cikin fadamar garin Durbawa. Shigarta fadama ke da wuya sai ta shiga wani wuri ta kafe cikin laka. Da baunan ya kafe cikin laka sai mutanen da ke biye da ita suka rinka yi masa kuwwa. Wannan kuwwa da suka yi masa ya tayar masa da hankali kwarai. Ganin ya kafe cikin laka sai wani mutum ya zo ya buge shi.

Nan da nan baunan ya sa kahonsa ya fasa wa mutumin da ya buge shi ciki da kaho. Bayan wannan kuma, mutum na biyu ya zo bugun sa suka sarke. Nan take kafin lokaci kadan, sai ga mutumin bisa kan baunan ya dauke shi yana yawo da shi. A cikin wannan hali mutane na kallo babu mai iya kawo agaji.

 

A karshe baunan ya kayar da mutumin kuma, ya lashi jikinsa. An ce idan bauna ta lashi jikin mutum sai kashi ya fito fili. Mutum na farko da ya bugi baunan lokacin da ya kafe cikin laka da na biyu da ya nuna bajinta suka sarke, duk sai da aka kwaso su aka kai asibitin garin Sakkwato. Da likita ya dubi mutum na farko ya ce ya rasu. Wasu suka nuna akwai sauransa bai mutu ba. Ga abin da Malam Kwasare ya ce a kan haka:

 

Durbawa da taz zaka tay yi gulbi,

Tay yi kafau ana kuwwa ga bauna.

 

Wani yaz zaburo har yab buge ta,

Sai tas sa kaho tah hude wanna.

 

Wani yaz zaburo sai sunka sarke,

Tad dauke shi sai bisa kanta bauna.

 

Tana yawo da shi abu babu kyawo,

Tak kashe shi tal lashe shi bauna.

 

Sakkwato anka kai su wurin tiyata,

Likita gudansu an ce babu wanna.

 

Bayan haka baunan ya baro can ya iso garin Basansan inda a tarar da wani jakin da ya kama murza sai da ya yi halinsa. Bayan ya kashe jakin sai ya ga wani yaro. Nan take baunan ya nuna wa yake so ba yaron ba? Daga nan ya biyo yaron aguje. Yaron na gudu baunan na biye da shi. Nasarar da yaron ya samu ita ce, samun ramin wata tsohuwar rijiya da ya yi ya fada ciki.

Da baunan ya ga bai sami sa’ar yaron ba, sai ya ga wani saurayi sai ya nufo shi. Da baunan ya tarar da saurayin sai ya kama murzar shi har ya mutu. Bayan saurayin kuma, sai mahaifinsa da ya ga barnar da baunan ya yi masa, ya ga ba ya iya kyale shi.

Da baunan ya kashe yaron sai ya shiga dawa. Mahaifin yaron na fitowa sai ya dauki sanda ya bi shi. Mutanen da ke wurin suka hana shi amma, ya ki. Da baunan ya kula da mutumin sai ya juyo zuwa gare shi. Baunan ya hau mutumin har sai da ya ga babu shi sannan ya daina. Duk abin da baunan ke yi wa mutumin jama’a na kallo amma, babu yadda za a yi domin kowa na tsoron ya same shi balle ya kai kansa ga halaka. Ga abin da Maharazu ya ce a kan haka:

 

Basansan da taz zaka tag ga jaki,

Tam milke shi nan taf fara banna.

 

Tam milke shi yam mutu babu wanna,

Yaro yag ganat tam kori wanna.

 

Suna ta gudu kwarai yaf fada rame,

Samun rijiya yab baude bauna.

 

Sai tat ta da kai tak koma doni,

Tac tcinkayi wannan tay yi cana.

 

Tad dauke shi tak kasai ga fili,

Tana murzas sa tak kasha saurayin na.

 

Ubanai yaf fito tak kama dawa,

Sai yab bi ta yag gwadi babu sauna.

 

Da sandatai mutane na hana mai,

Shina tafiya shina tasam ma bauna.

 

Da tatc tcinkai shi sai taz yo gare shi,

Tak kasai tana murza ga gona.

 

Tana murzash shi kowa na ganin su,

Nan aka gane talitta ta bauna.

 

Bayan duk wadannan abubuwa da suka faru an sami jin cewa, baunar ta hadu da wata tsohuwa da ta je daji domin samo karan makamashi. Tsohuwa na kayan karanta sai baunan ya kwashe ta har karanta ya koma kansa. Tsammanin bauna tsohuwar ce yake murza. Nasarar da tsohuwar ta samu ita ce, murzan da baunar ta yi ta yi wa kara tana tsammanin tsohuwar ce. Ita kuma tsohuwa, da ganin baunan ya amshe karan sai ta yi ta kanta ta ruga har ta sami tserewa. A kan haka ne Malam Maharazu ya fadi cewa:

Akwai wata mace ta dauko karanta,

Tana tafiya suke gamuwa da bauna.

Sai tas sa kaho tas sa cikinta,

Karan nan sunk azan matashi ga bauna.

kaho si yash shige ga karan ga nata,

Kara sai sunka zan bias kai na bauna.

Dada kafin ta warwatce karan nan,

Maccen tana gudu tac tcar ma bauna.

Bayan rabuwar tsohuwar da baunan sai aka sami wani maharbin tsuntsaye ya zo yana tsammanin yadda yake yi wa tsuntsaye haka ake yi wa bauna. Da isowarsa sai ya yi wa bindigarsa duri. Yana regon bauna babu ko natsuwa sai ya harbe shi. Da baunan ya zaburo zuwa gare shi, sai ta hau shi har ya mayar da shi gawa. Ganin yadda maharbin ya zo da rawar jiki yana harbin bauna, mutanen suka yi tsammanin ba ya da lafiya, tababbe ne, wasu kuma suka ce ba komai ba ne sai yawan kwankwaman da ke ga baunan.

Da aka tabbatar da mutuwar mutumin, sai mutane suka kama kansu daga baunan ganin buwayar da yake da, da kashe mutane da yake yi. Wadanda bauna ya kashe aka yi wa kowa kabari aka sa aka rufe.

Duk da rufewar da aka yi musu sai da hukuma ta sa aka tone kaburburan aka ciro matattun aka sa likita ya auna domin a binciki sanadin mutuwarsu. Bayan likita ya auna sai ya gano akwai alamun kashin bauna a jikinsu wanda ake kyautata zaton shi ne ya hallaka su.

Da wannan muka kawo karshen tarihin da aka samu a cikin “Wakar bauna” wadda Malam Maharazu Barmu Kwasare ya wallafa. Allah Ya ji kan wadanda suka mutu sanadiyyar baunar tare da fatan ka da Allah ya maimaita, amin.