✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shari’ar Batanci: An jibge jami’an tsaro a kotu

Kotu na sauraron daukaka karar wadanda aka yanke wa hukunci a Kano.

An tsaurara matakan tsaro a kotun da ke sauraron shari’ar batanci ga Manzon Allah (SAW) da ake zargin wasu matasa biyu da yi a Jihar Kano.

An girke jami’an tsaron ne yayin da Kotun Daukaka  Kara a jihar ke sauraron daukaka karar da matasan suka yi kan hukuncin da Babbar Kotun Musulunci ta yanke musu.

A ranar Alhamis kotun ke ci gaba da sauraron shari’ar bayan lauyoyin masu kalubalantar hukuncin kotun Musuluncin, kasancewar lauyoyinsu ba su samu halartar zaman da aka yi sakamakon tarzomar zanga-zangar #EndSARS ba.

Shari’o’in sun hada da na Aminu Yayaha Sharif wanda Babbar Kotun Shari’ar Musulunci ta yanke wa hukuncin kisa ta hanyar rataya saboda yin batanci ga Manzon Allah (SAW).

Na biyu shi ne na wani mai suna Umar Faruk mai shekara 13 da kotun Musuluncin ta yanke masa hukuncin daurin shekara 10 a kurkuku shi ma saboda batancin.

A zaman kotun na watan Oktoba, lauyoyin matasan sun shaida wa kotun ta bakin Zubairu Suleiman Usman cewa zanga-zangar EndSARS ta hana su baro Legas zuwa Kano halartar zaman kotun.

Zubairu wanda ba lauya ba ne ya ce wa kotun cewa lauyoyin ne suka sanar da shi haka, suna kuma rokon a sanya ranar sauraron shari’ar zuwa tsakanin 26 da 30 ga watan Nuwamba.

Daga nan alkalin kotun ya amince da bukatarsu ya kuma sanya 26 watan Nuwamba don ci gaba da shari’ar, bisa la’akari da girman shari’ar da kuma yadda zanga-zangar ta EndSARS ta tayar da hankula a sassan Najeriya.