Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Shari’ar Buhari da Atiku kotu zata yanke hukunci yau

A yau Laraba kotun sauraron kararrakin zabe ke yanke hukunci a kan karar da Atiku Abubakar na jam’iyyar PDP ya shigar a gabanta don kalubalantar zaben Shugaba Muhammadu Buhari na jam’iyyar APC bayan zabensa da aka yi a matsayin shugaban Najeriya.

Atiku Abubakar ya shigar da karar ne bayan da hukumar zaben kasar INEC ta bayyana Shugaba Buhari a matsayin wanda ya ci zaben ranar 23 ga watan Fabrairun 2019.

ADVERTISEMENT