✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shari’ar da ba na mantawa – Bulkachuwa

Shugabar Kotun Daukaka Kara da ta yi ritaya a makon jiya Mai Shari’a Zainab Bulkachuwa, wadda ita ce mace ta farko da ta shugabanci kotun…

Shugabar Kotun Daukaka Kara da ta yi ritaya a makon jiya Mai Shari’a Zainab Bulkachuwa, wadda ita ce mace ta farko da ta shugabanci kotun ta shaida wa Sashin Hausa na Gidan Rediyon BBC cewa ba ta taba yanke hukuncin kisa ba a tsawon shekarun da ta yi tana aiki.

Mai shari’ar Zainab Bulkachuwa ta kuma ce shari’ar da ta tsaya mata a rai ita ce ta wata yarinya da aka yi wa fyade a lokacin tana shari’a a Babbar Kotun Jihar Bauchi.

“Shi wanda ya yi wa yarinyar fyaden matashin lauya ne, kuma na tabbatar da laifi a kansa har ma na yanke masa hukuncin daurin shekara 15 a gidan yari. Daga nan ya daukaka kara zuwa Kotun Daukaka Kara a Jos a lokacin Mai Shari’a Maryam Alooma na kotun; ita ma ta tabbatar da hukuncin nawa. Amma da aka kai batun Kotun Koli da yake lokacin duk maza ne a wajen sai suka ce a’a, ai don mu mata ne shi ya sa muke tausayin yarinyar amma ya kamata a duba lamarin lauyan tun da yaro ne, hukuncin na iya katse masa burinsa na daukaka a aikinsa,” inji ta.

Ta ce “To gaskiya wannan abu ya kada ni sosai. Don haka a ganina, mafi yawancin shari’o’in fyade ana yi wa matan rashin adalci sosai, saboda rashin isassun shaidu ko rashin zuwa asibiti da cewa yawanci lauyoyin da ke shari’ar fyade maza ne da kuma tsoron kyama da iyaye ke yi.”

Ta ce akwai kuma shari’ar tsohon Gwamnan Jihar Filato Joshua Dariye a 2007, wacce mutum takwas daga Majalisar Dokokin Jihar suka tsige shi.

“Amma na yanke hukunci cewa ba su bi doka da tsari ba don haka abin da suka yin bai tabbata ba,” kamar yadda ta shaida wa BBC.