✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shari’ar Maryam Sanda ta samu tsaiko

A shekaranjiya Laraba ce aka sake hallara kotu, domin ci gaba da shari’ar Maryam Sanda, wacce ake tuhuma da kashe mjinta mai suna Bilyaminu Bello…

A shekaranjiya Laraba ce aka sake hallara kotu, domin ci gaba da shari’ar Maryam Sanda, wacce ake tuhuma da kashe mjinta mai suna Bilyaminu Bello a bara, inda ba a samu damar ci gaba da shari’ar ba bisa dalilin rashin zuwan alkalin kotun.

Maryam Sanda, tana fuskantar shari’a ce a wata Babbar Kotu da ke Unguwar Maitama Abuja, bisa zarginta da kashe mijinta, Bilyaminu, wanda da ne ga tsohon Shugaban Jam’iyyar PDP na Kasa, Alhaji Bello Halliru.

Tun farkon shari’ar an gurfanar da Maryam tare da yayanta, Aliyu Sanda da mahaifiyarta Maimuna Aliyu da ’yar aikin gidansu mai suna Sadiya Aminu, wadanda aka zarga da cewa sun taimaka mata wajen boye wasu abubuwa da suka dangance kisan, suka kau da su daga wurin da al’amarin ya faru. Dukansu dai sun musanta aikata laifin.

A can baya, ’yan sanda, wadanda su ne masu shigar da kara, sun gabatar da shaidu shida, wadanda za su tabbatar da cewa lallai wadanda ake tuhumar sun aikata laifin. An kai ga lokacin da lauyan mai gabatar da kara ya bukaci rufe batunsa, sai lauyan Maryam, Olusegun Jolaawo ya bayyana wa kotun cewa yana da niyyar ya gabatar wa kotu matsayarsu ta cewa Maryam ba ta aikata laifin da ake tuhumarta ba. Wannan dalili ne ya sanya aka dage shari’ar zuwa shekaranjiya Laraba, domin lauyan ya gabatar da bukatarsa a rubuce.

Wannan bukata da lauyan Maryam zai gabatar, tana nufin cewa bisa ga shaidun da lauyan mai gabatar da kara ya bayyana wa kotu, ba su gamsar sosai ba, don haka hujjojinsu ba su da karfin da za su isa a tuhumi Maryam da kisan mijinta.

Idan har wannan bukata ta lauyan Maryam ta samu nasara, to abin da zai biyo baya shi ne, kotu za ta sallame ta, ma’ana ba za a hukunta ta ba. Amma idan har bukatar ba ta samu wucewa ba, to kotu za ta nemi lauyanta da ya shirya kariya daga tuhumar da ake yi mata, bisa hujjoji da shaidun da masu tuhuma suka gabatar wa kotu.

Sai dai bayan da dukan sassan shari’ar suka hallara a kotun a shekaranjiya Laraba, an shaida musu cewa Alkalin Kotun, Mai shari’a Yusuf Halilu ba ya nan, ya tafi wani aiki na musamman. A dalilin haka aka dage shari’ar zuwa ranar 26 ga watan Maris din nan domin ci gaba da shari’ar.