✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shari’ar zabe: Buhari ya doka Atiku da kasa

Zan je Kotun Koli – Atiku Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC ya samu nasarar kayaR da Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP a shari’ar…

  • Zan je Kotun Koli – Atiku

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC ya samu nasarar kayaR da Atiku Abubakar na Jam’iyyar PDP a shari’ar da aka shafe wata shida ana tafkawa ka zaben Shugaban Kasa na bana.

Sai dai Atiku da jam’iyyarsa ta PDP sun ce  za su kalubanci hukuncin da Kotun Zaben Shugaban Kasar a Kotun Koli. Kotun  a zaman yanken hukuncin da aka shafe awa takwas ana karanto bayanan hukuncin ta bai wa Shugaba Muhammadu Buhari nasara a kan abokin takararsa, Atiku Abubakar na PDP.

Kotun Zaben Shugaban Kasar, ta kori daukacin karar da Atiku da PDP suka shigar suna kalubalantar zaben da Hukumar INEC ta bayyana cewa Buhari na APC ne ya yi nasara.

Cikin batutuwan da kotu ta yi watsi da su har da batun zargin an gudanar da zabe a yawancin wurare ba bisa ka’idar da dokar zabe ta shimfida ba, sai zargin magudi a jihohin Borno, Yobe, Neja, Katsina, Bauchi, Jigawa, Kaduna, Kano, Gombe da kuma Kebbi. Atiku da PDP sun yi zargin cewa an yi amfani da kudi da  karfin jami’an tsaro a zaben, sannan an samu rikice-rikice da tashe-tashen hankula da sauran batutuwan da kotu ta ce duk PDP da Atiku sun kasa gamsar da kotun kan zarge-zargen da suka yi.

Alkalai biyar da suka gudanar da shari’ar, a karkashin jagorancin Mai shari’a Mohammed Garba sun yi ittifaki kan yi watsi da karar.

A yayin karanto hukuncin Mai shari’a Mohammed Garba ya ce masu kara sun kasa gabatar wa  kotu hujjojin da za ta gamsu da su, don haka ta yi fatali da karar. Ya ce Atiku da Jam’iyyar PDP su kasa gabatar da shaidu daga wadancan jihohi 11 da suke zargin an yi aringizon kuri’u, kamar yadda yake a sashi na 15 cikin karar da aka shigar.

Game da batun takardun shaidar kammala karatun Shugaba Buhari da kuma bayanan karya da ke cikin karar, bisa sashi na 131 na kundin mulkin kasar nan a kan lamarin ilimi, sashin ya ce mutuum kan iya gabatar da takardun shaidar iliminsa na kammala makaranta, wanda Buhari ya tabbatar ya halarci sakandare a Katsina, kuma ya gabatar da shaidar WEAC da bayanin jarrabawarsa ta Cambridge, kuma korafin bai hada da satifiket ba wajen cike takardar hukumar zabe mai lamba (CF001), wannan ba dole ba ne karkashin sashi na 131 da 137 da kuma na 138 (1) da na (b).

Ya ce ba Buhari ne yake yi satifiket din ba, kuma mai kara ba zai zargi Jam’iar Cambridge ko WAEC cewa suna da sha’awa a cikin batun ba.

Kotun ta kuma ce karar da PDP ta shigar dangane da takardun shaidar karatun Shugaba Buhari, batu ne na kafin zabe, ba bayan an rigaya an yi zabe ba.

Kan cewa Buhari bai samu yawancin kuri’un da aka kada ba, kotun ta ce shaidu 62 da mai karar ya gabatar da suka hada da Osita Chidoka sun gaza bayar da bayanai kan sahihancin rumbun tattara sakamakon zabe ta INEC, sai dai sun ta’allaka ne kan bayanai da Shugaban Hukumar Farfesa Mahnood Yakubu da Ministan Jiragen Sama da kuma taron manema labarai da Babban Kwamishinan Hukumar Zabe Festus Okoye suka yi.

Alkalin ya ce dogaron da manazarcin bayanan kwamfuta dan Kenya Dabid Ayu Njorga da ya samo daga wata kafa mai suna www.factsdontlie.com ta wani mai kwarmatawa  na Hukumar INEC ne aka yi amfani da shi wajen kafa hujja da adadin da Atiku ya gabatar na kuri’a miliyan 18 da 356 da 732  Buhari kuma miliyan 16 da dubu 741 da 430,  abu ne da babu sashihanci. Kotun ta ki amincewa da kalubantar rashin shigar da sunan Mataimakin Shugaba Kasa Yemi Osinbajo, inda ta ce ai zaben ba a kan Osinbajo yake ba, a kan Buhari da kuma jam’iyyar da Buhari ke wakilta ne. Don haka babu wata damuwa ko kuskure don babu sunan Osinbajo a cikin wadanda ake kara.

Hakazalika PDP ta zargi Babban Hafsan Soji da Sufeto Janar na ’Yan sanda da Darakta Janar na Hukumar tsaro ta DSS cewa sun taka muhimmiyar rawa wajen tayar da yamutsi a lokacin zaben. Bisa dalilin rashin kawo shaidu a kan hakan sai, kotun ta cire jami’an tsaro daga cikin wadanda ake zargi.

Hukumar zaben ta ce wannan batu bai kamata ya shigo a cikin wannan kara ba, kamata ya yi a ce tun kafin zabe PDP ya kamata ta kai batun kotu.

PDP ta tsaya kai da fata cewa Buhari bai cancanci tsayawa takara ba, domin ba ya da mafi karancin takardun da doka ta tanada na ya tsaya takarar Shugaban Kasa da su.

Wadannan na daga cikin batutuwa da yawa da PDP ta yi amfani da su ta kai hukumar zabe, Buhari da APC a kotu.

Sai dai kuma Shugaban Kotun, ya yi amfani da Sashin na 138 (1) na Dokar Zabe, inda ya ce sashin ya amince mai kara ya shigar da karar zargin abin da ya shafi gabatar da bayanai na karya ga Hukumar INEC.

Mai shari’a Garba ya ce don haka kotu za ta duba sahihanci ko akasin abin da ake kara akai.

Sauran alkalan kotun hudu sun amince da wannan bayani.

Atiku da PDP ba su yi nasara a kan bukatu biyar da suka roki kotun ta biya musu ba.

Sai dai Lauyan Atiku da kuma Jam’iyyar PDP Mike Ozekhome (SAN) ya ce akwai kura-kurai da dama a cikin hukuncin, wadanda suka hada da rashin bin ka’idojin jin ta bakin shaidu da rashin bin tsarin gabatar da shaidun, kamar yadda masu shigar da kara suka bukata. “Kuma an yi son rai wajen bin tsarin Dokar Zabe, don haka akwai bukatar mu sake daukaka kara, wanda muna da yakinin a Kotun Koli za ta saurari korafe- korafenmu. Babu tantanma za mu daukaka kara,” inji shi.

Shugaban Jam’iyyar PDP ta Kasa Uche Secondus cewa ya yi lauyoyin jam’iyyar za su duba wannan hukunci cikin tsanaki, kuma su san matakin da za su dauka.

Nasarar ’yan Najeriya ce                     – Buhari

Da yake tsokaci a kan hukuncin, Shugaban Kasa Muhammadu Buhari cewa ya yi wannan nasarar da ya samu ba tasa ba ce kawai, ta al’ummar Najeriya ce, wadanda suka fito kwansu da kwarkwatarsu su zabe shi a karo na biyu. Ya ce “Ina da yakinin jama’ar kasar nan sun yarda da abin da nake yi wa al’ummar kasar nan.” Shugaban kasar ya bayyana hakan ne ta bakin Kakakinsa Mista Femi Adesina. Ya kara da cewa wannan nasara daga Allah take kuma ya yaba wa bangaren shari’a kan yadda suka zartar da hukunci babu sani ko sabo. Shugaba Buhari ya yi kira ga wadanda ba su yi nasara ba su zo a hada hannun domin ci gaban kasar nan da kuma tsarin dimokuradiyya. Buhari ya ci gaba da cewa da yanke wannan hukunci lokaci ne da kasar nan za ta samu ci gaban da aka dade an bukatarsa, don haka kamata ya yi a mance da duk wani abu da ya wuce a zo a gina kasa domin ci gaban al’ummar kasar nan.

Tinubu da Lawan sun taya Buhari murna

Shugaban Majalisar Dattawa Ahmad Lawan ya taya Shugaba Buhari da Jam’iyyar APC  murnar nasarar da suka samu. Ya ce hakika sashin shari’a ya saka wani babban tarihi wajen yin adalci a kan bai wa al’ummar kasar nan abin da suka zaba a zaben da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu. Lawan ya bayyana hakan ne ta bakin Kakakinsa Ola Awoniyi. Shi ma Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila da Mataimakinsa Ahmad Wase aun taya Shugaba Buhari murnar nasarar da ya samu. Kakakin Shugaban Majalisar, Lare Lasisi ya ruwaito Gbajabiamila yana jinjina wa sashin shari’a musamman alkalan da suka jagoranci zaman kotun kan kyakyawan aikin da suka yi. Shugaban ya mika sakon taya murna ga dukkan ’ya’yan Jami’yyar APC kan wannan nasara da jam’iyyar ta samu.

Shi kuwa jagoran APC na Kasa, Sanata Ahmed Bola Tinubu taya murna ya yi ga Shugaba Buhari, ya ce hakika sashin shari’a ya taka muhimmiyar rawa wajen ceto tsarin dimokuraddiya a kasar nan.

Sauran wadanda suka taya Shugaba Buhari murna sun hada da gwamnonin jihohin Kebbi Atiku Bagudu da Godwin Obasaki na Edo da Dapo Abiodun na Ogun da Yahaya Bello na Kogi da Babajide Sanwo-Olu na Legas da Gwamnan Jihar Ribas Nyesom Wike na Jam’iyyar PDP.