✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shari’ar zaben Gwamnan Kano, Sakkwato: A yau kotu za ta yanke hukunci

A ci gaba da sauraran kararrakin zaben Gwamnonin jihohin Kano da Sakkwato, bayan kotunan sun gabatar da korafin da jam’iyyun adawa suka gabatar na kalubalatar…

A ci gaba da sauraran kararrakin zaben Gwamnonin jihohin Kano da Sakkwato, bayan kotunan sun gabatar da korafin da jam’iyyun adawa suka gabatar na kalubalatar nasarar zaben Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da Aminu Waziri Tambuwal.

Wadannan jihohin biyu dai sun kasance suna da jam’iyyu adawa da suka dage akan har sai kotu ta bi masu hakkinsu na zaben Gwamnonin jihohin.

A jihar Kano dan takarar PDP Injiniya Abba Kabir Yusuf, na kalubalantar nasarar zaben Gwamna Ganduje na jam’iyyar APC. Yayin da a jihar Sakkwato dan takarar Gwamnan jihar na APC Ahmed Aliyu, ke kalubalantar zaben nasarar Gwamna Tambuwal na jam’iyyar PDP.