Da Dumi Dumi

Shari’un Zabe: Ta leko ta koma wa Ihedioha na Imo

  • Yau Gwamnan Bauchi zai san matsayinsa
  • Gwamnonin Kano da Sakkwato kuma ranar Litinin

Ta leko ta koma wa tsohon Gwamnan Jihar Imo Emeka Ihedioha na Jam’iyyar PDP bayan da Kotun Koli ta yanke hukuncin soke zabensa tare da tabbatar da Sanata Hope Uzodinma na Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe Gwamnan Jihar Imo a zaben ranar 9 ga watan Maris din bara.

Kotun wadda ta kunshi alkalai bakwai a karkashin shugabancin Babban Jojin Najeriya, Mai shari’a Tanko Muhammad ta tabbatar da cewa ba a zabi Ihedioha ta sahihiyar hanya ba, ko wanda ya fi cin kuri’un da aka kada a zaben da aka gudanar.

Don haka kotun ta bayar da umarni ga Hukumar Zabe ta Kasa ta karbe takardar shaidar zama Gwamna da ta ba tsohon Gwamna Ihedioha ta mika wa sabon Gwamna Hope Uzodinma wanda shi ne sahihin wanda ya lashe zaben. Kuma “A rantsar da shi a matsayin Gwamnan Jihar Imo ba tare da bata lokaci ba.”

Da take karanta hukuncin, Mai shari’a Kudirat Kekere-Ekun, ta bayyana amincewar kotun kan tabbatar da sahihancin wasu kuri’u da Uzodinma ya ci a mazabu 388 a fadin jihar, inda ya samu kuri’a dubu 213 da 695.

Babbar Jam’iyyar hamayya PDP ta ce ta kadu kan hukuncin Kotun Koli kan zaben Gwamnan Jihar Imo. Sanarwar da Kakakin Jam’iyyar Kola Ologbondiyan ya fitar bayan  yanke hukuncin ta ce, PDP ta kasa fahimtar dalilan da Kotun Koli ta dogaro da su na yanke hukuncin.

ADVERTISEMENT

“PDP ta kasa fahimtar yadda za a ce dan takarar da ya zo na hudu a zaben Gwamna na ranar 9 ga Maris da kuri’a dubu 96 da 458 a ce ya doke dan takarar PDP da ya samu  kuri’a dubu 276 da 404

PDP ta ce an sauya wa mutanen Imo wanda suka zaba aka ba wanda mutanen jihar ba su ra’ayinsa a zaben da aka gudanar. Ta ce yanzu duk nasarori da ci gaba da kuma kwanciyar hankali da aka samu a kakashin Gwamna Emeka Ihedioha ya tafi a banza.

Kamar yadda BBC ya ruwaito, Jam’iyyar PDP ta yi kira ga magoya bayanta a Jihar Imo su kai zuciya nesa tare da rungumar kaddara kan hukuncin kotun.

A nata bangaren, Jam’iyyar APC ta bayyana farin cikinta da hukuncin Kotun Kolin da ya bayyana dan takararta Hope Uzodinma a matsayin wanda ya lashe zaben Gwamnan Imo.

APC ta ce duk da cewa ta yi mamakin yadda ta rasa kujerar Gwamna a Jihar Zamfara a Kotun Koli da kuma yadda kotun ta haramta mata shiga zabe a Ribas amma hakan bai sa ta cire tsammani ba a kotun.

A yau ne ake sa ran Kotun Kolin za ta yanke hukunci kan zaben Gwamnan Jihar Bauchi tsakanin Gwamna Bala Mohammed na PDP da tsohon Gwamna Mohammed Abubakar na APC. Sai kuma a  ranar Litinin mai zuwa ta yanke hukunci a kan shari’ar  Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar PDP da  Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano na Jam’iyyar APC.

Lauyoyin bangarorin da suke shari’ar sun tafka muhawara kafin alkalan su dage zaman. sauraron kararrakin zaben jihohin Bauchi da Sakkwato da Benuwai da Filato.

A ranar Litinin ce kotun ta fara zama kan shari’o’in amma sai aka dage zaman zuwa Talata saboda abin da ta kira “rashin lafiyar” daya daga alkalai bakwai da za su yanke hukunce-hukuncen.

Share