Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Sharu Rabi’u Usman Baba ya fi kowa daukaka a yabon Annabi – Amininsa

A ranar Alhamis din makon jiya ce Allah Ya yi wa fitaccen mawakin yabon Annabi Muhammad (saw), Sharu Rabi’u Usman Baba rasuwa, bayan da ya yi fama da ’yar gajeruwar jinya.

Marigayin mai shekara 52, ya rasu ne a gidansa da ke Unguwar Janbulo da ke yankin Karamar Hukumar Gwale, Jihar Kano.

ADVERTISEMENT

An haifi marigayi Sharif Rabi’u Usman Baba a Unguwar Gwammaja a birnin Kano. Ya yi karatunsa na Islamiyya da boko a nan Unguwarsu Gwammaja.

Ya fara kasidar yabon Annabi Muhammadu (saw) tun a lokacin yana koyarwa a Makarantar Islamiyyarsu kafin daga bisani abin ya bunkasa ya zama babban sha’iri a wannan fage, wanda a rasuwarsa ya zama shi ne Shugaban Kungiyar Ahbabu Rasulullah.

ADVERTISEMENT

Wannan fice da ya yi a harkar yabon Manzon Allah (saw) shi ya jawo masa daukaka har ma ya kai yana zuwa tarukan majalisi da akan shirya a lokutan maulidi ko kuma a wasu taruka daban-daban.

Marigayi Sharu Rabi’u Usman Baba ya yi wakoki da dama wadanda suka hada da “Tsumagiya” da “Zuma” da “Salka” da “Bege” da “Isra’i” da “Bege Dadi” da sauransu.

Malam Nasiru Abdulhamid Dantata, babban amini ne ga marigayin. Ya bayyana rasuwar marigayin da babban rashi ba gare su kawai ba har ga duniya baki daya; musamman masoya Manzon Allah (saw).

Ya bayyan marigayin a matsayin mutum mai saukin hali da tausayi da son zumunci. “Shi Malam Rabi’u tun muna yara ba shi da abokin fada. Yana da hakuri da kawaici, ya kasance mu za mu yi masa laifi amma shi zai ba mu hakuri don son a zauna lafiya. Ba zan ce ba mu samun sabani a kan wasu abubuwan ba, amma a wasu lokutan za mu zauna mu sulhunta junanmu. Ban taba gaya masa ga abin da zai yi a duniya ya yi mini musu ba. Duk da cewa ya sami daukaka amma hakan bai sa ya zama mai girman

kai ba. Mutum ne mai farin jini. Za a tara sha’irai masu yawan gaske amma da Malam Rabi’u ya zo wurin shi ke nan sai kallo ya koma kansa.

“Idan ya je wuri abin da ya fada ko na minti goma ne ya gamsar da mutane. Mun sha tafiya wuri za ka ga tafiya ba ta fi ta minti biyu ba amma sai mu kai awa biyu muna yi saboda jama’a. Wani ma so yake ko rigar Malam Rabi’u ya taba, gani yake ya ishe shi ba don komai ba saboda ya rike Manzon Allah (saw). A kan wannan tafiya ya gudanar da rayuwarsa kuma a kanta kuma ya rasu,” inji Malam Nasiru.

Da yake tabo tarihin yadda marigayin ya fara wakokin yabon Annabi, Malam Nasiru ya bayyana cewa marigayin ya fara waka tun yana dan shekara 14, a lokacin da yake koyarwa a makarantar Islamiyya, wanda kuma Allah Ya daukaka shi.

“Zan iya tunawa, tare muka faro wannan harkar da su Khamsusi Bala Maiyafe da Malam Karami amma cikin ikon Allah Malam Rabi’u ya fi mu samun daukaka a harkar. Zan iya tunawa daukakar Malam Rabi’u a fagen yabon Annabi ta fara ne tun daga lokacin da ya yi wata waka wacce ake mata lakabi da “Yan Kwadi” kimanin shekaru 40 da suka gabata. An sami wannan lakabi ne daga ’yan amshinsa wadanda a wancan lokacin yara ne kanana yake zaunar da su. A lokacin ma ba a amfani da mandiri amma wadannan ’yan amshin suna yin aikinsu cikin salon birgewa da sha’awa. To tun daga wannan lokaci sai likkafarsa ta rika ci gaba, ya zama cewa idan zai yi majalisi mutane sukan taru kamar za su tsage.

“Haka kuma Mauludin makarantarsu ya fi kowane mauludi da ake yi a Kano cika saboda mutane sun san zai yi sabuwar waka a wurin. Haka abubuwa suka ci gaba da faruwa har zuwa lokacin da muka kafa wata kungiya ta Jama’atul Ahbabu Lilnabiy Awwab, wadda Malam Sadi ’Yantandu ya shugabanta, yayin da shi Malam Rabiu ya zama mataimakin shugaba. Mun sami kamar shekara 20 muna gudanar da kungiyar, inda muka kafa rassa masu yawa a fadin kasar nan. Amma daga baya kowa ya janye sai aka bar Malam Rabi’u kadai. Shi ya rungumi kungiyar ya ci gaba da aiwatar da ita.”

Aminin nasa ya ci gaba da cewa “kai sai da ya dauki shekara 39 yana zagaya Najeriya. Duk garin da ake da al’ummar Hausawa, to Malam Rabi’u yana da Halifa a wurin.”

A cewarsa wani abu da ba zai manta da shi ba shi ne, kwana bakwai kafin rasuwar marigayin, sun gudanar da majalisi a garin Dambatta. Ya ce a wannan rana sun gudanar da majalisin da ba su taba yin irinsa ba a garin.

“Kasancewar Allah Ya yarda zai yi wannan majlisi, ni na karfaf masa gwiwa a kan sai mun yi majalisin a waccan ranar, domin shi ya so a bari sai bayan Sallah. A nan nake gaya masa cewa ai bayan Sallar ba a hannunmu take ba. Har na kara gaya masa cewa ya kamata mu yi majalisin na musamman ganin cewa idan aka fara azumi ba lokacin majalisi. Haka ya amince na kira mutanen da za mu je wurinsu na gaya musu cewa idan za su ba mu wurin kwana Malam Rabi’u zai baje musu kolin yabo, cikin farin ciki suka amince. Haka kuwa aka yi, muka shirya muka je garin nan muka yi musu majalisi har zuwa wayewar gari sannan muka dawo gida. Babu shakka wannan lokaci mun yi zantuttukan da ba mu taba yi ba. Wannan shi ne ganina da shi na karshe. Sai dai mu yi masa addu’ar Allah Ya jikansa, Ya yi masa rahama.”

Malama Zainab Rabi’u ita ce uwargidan marigayi Sharu Rabi’u. Ta bayyana halayyarsa da cewa mutum ne na kwarai wanda ya iya zama da jama’a. “Yau kimanin shekara 21 muke tare da shi amma dadai da rana daya ba mu taba sa-in-in-sa da shi ba. Babu shakka mun yi rashi sai dai muna yi masa addu’ar samun dacewa da rahamar Allah.”

Ita ma Malam A’isha Munnubiya ita ma matar marigayin ce kuma ta bayyana rasuwar mijin nata a matsayin gibin da cike shi zai yi wahalar gaske. “Shi miji ne da yake kulawa da iyalansa. Ba mu kadai ba, duk wanda ya kusance shi ya san wannan. Babu shakka ya yi iya kokarinsa wajen ganin ya kyautata mana. Allah Ya jikansa, Ya kyautata makwancinsa.”

Aminiya ta gana da wasu daga cikin ’ya’yan marigayin da a yanzu haka suka gaje shi a sha’anin da aka san shi a kai na yabon Annabi. ’Ya’yan sun hada da Nura da Hassanu da Ka’ab da sauransu. Sun bayyana rasuwar mahaifin nasu a matsayin rashi babba a gare su wanda suka yi masa fatan samun rahama.

“Dukkaninmu muna yin wakokin yabon Annabi (saw), kasancewar mun taso mun ga mahaifinmu a cikin  wannan hidima; to hakan ya sa mu ma muka tashi da son Annabi (saw) da kuma yin yabo a gare shi. Kowane daga cikinmu idan ya rubuta kasidarsa yana kai masa don ya duba ta. Idan zai yi gyara sai ya yi, idan kuma ba gyara sai ya sanya albarka.”

A nata jawabin game da rasuwar mahaifin nata, babbar diyar marigayin mai suna Humaira Sharu Rabi’u ta bayyana cewa rasuwar mahaifinta ta girgiza ta, musamman idan ta tuna maganarsu ta karshe da shi, inda ya umarce ta da ta zauna da mijinta lafiya tare da rike kannenta hannu biyu.

“Abin da ya tsaya mini a rai shi ne, lokacin da na zo duba shi a daren da zai rasu; har zan fita sai ya kira ni ya zaunar da ni ya rika yi mini nasiha cewa in zauna da mijina lafiya. Ya ce in rike aurena, ya kuma yi mini nasiha cewa ni ce babba don haka in yi kokarin hada kan ’yan uwana. Har kuma yana gaya mini cewa watakila wannan haduwar tamu ita ce ta karshe. Ashe kuwa hakan ne.”

Marigayi Sharu Rabi’u Usman Baba ya rasu ya bar matan aure uku da ’ya’ya 18 da jikoki 4. Tuni dai aka yi jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tanada.