✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shawara ga Gwamnatin Zamfara

Shekarar 2019 tana da matukar tasiri a tarihin Jihar Zamfara, domin a cikinta ce Allah Ya nuna karfin ikonSa ga mutanen da ke ganin jama’a…

Shekarar 2019 tana da matukar tasiri a tarihin Jihar Zamfara, domin a cikinta ce Allah Ya nuna karfin ikonSa ga mutanen da ke ganin jama’a ba su iya komai a siyasa. Ina fata abin da ya faru da su zai zama darasi gare mu baki daya, mu fahimci cewa ba a wasa da Allah (SWT) a cikin kowane lamari. Haka, a cikin shekarar ce fuskar siyasar jihar ta canja inda aka samu bullar sabon limamin canji (Sanata Kabiru Marafa) da kuma sabuwar gwamnati wacce Allah (SWT) Ya kawo, wadda ta kamata ta canja yanayi da kuma halayyar al’ummar jihar nan.

Abin da ya dace gwamnati ta lura a wadannan bangarori su ne;

  1. Ilimi: A gyara bangaren ilimi wanda gwamnatin baya ta lalata. Ta hanyar gyara tsarin karantarwa da samar da tallafin koyarwa a makarantu, wajen yi wa malamai horo lokaci zuwa lokaci da gyara albashinsu da sa ido a kai-a kai kan yadda malamai ke karantarwa tun daga firamare har zuwa sakandare. Amma gyare-gyare ko gine-ginen makarantu kawai ba su za su gyara fannin ilimi ba.

Sannan a daina ba yara kwai musamman wadanda suke makarantun jeka-ka-dawo, a yi amfani da kudin da ake kashewa wurin sayen kwan a yi musu kayan makaranta da kuma saya musu littattafan karatu “Tedt books” na muhimman darussan da suka kamata a ce kowane dalibi ya mai da hankali a kansu (Ingilshi da Lissafi). Haka a gina makarantun Tsangaya/Islamiyya a kowace mazaba da ke jihar nan tare da saka malaman addini kwararru a ciki. Wannan zai taimaka wurin rage yawan yaran da ke shigowa gari da sunan neman ilimin addini.

  1. Lafiya: Akwai bukatar gina dakunan shan magani a kauyuka tare da saka kayan aiki da kuma kwararrun ma’aikatan lafiya domin rage yawan matan da ke mutuwa wurin haihuwa da rage yawan masu mutuwa sakamakon kananan cututtukan da ke addabar mutanen karkara. Sannan dukkan manyan asibitocin da ke kananan hukumomi 14 a sake dubawa tare da gyara matsalolin da suke damunsu.
  2. Tattalin Arziki: Gwamnati ta yi amfani da ma’adinan da ke akwai a jihar nan wurin gina tattalin arzikin al’ummar jihar ta hanyar gina hanyoyi a kauyuka da samar wa kauyukan ruwan sha da wutar lantarki da wuraren koya wa matasa sana’o’in hannu a kowace mazaba ko karamar hukuma domin rage zaman banza da kuma kara yawan masu dogaro da kansu. Haka gwamnati ta ba harkar noma fiffiko bisa la’akari da dimbin arzikin da ake samu a harkar ta hanyar samar da iri da taki a kan lokaci ga manoma. Sannan a saka matasa a cikin harkar noma domin a Jihar Zamfara akasarin matasanmu ba su san muhimmancin noma ba, matasa a jihohin Katsina da Jigawa sun fi mu sanin muhimmancinsa.

4.Tsaro: Gwamnati ta dauki matakan ba-sani-ba-sabo a harkar tsaro ta hanyar cire siyasa. Duk wanda aka samu da hannu wurin kawo cikas ga zaman lafiya ko wane ne a yanke masa hukunci daidai da laifinsa don haka ya zama izina ga wadansu. Don haka ya kamata a samar da shawarwarin da ke cikin rahoton kwamitin tsaro a karkashin tsohon Sufeto Janar na ’Yan sandan Najeriya na M.D Abubakar. Sannan duk da cewa an yi sulhu akwai bukatar baza isassun jami’an tsaro a dukkan sassan jihar nan da ke fuskantar barazanar tsaro domin dakile yunkurin duk wani mai niyyar lalata sulhun da aka yi.

Idan gwamnatin Jihar Zamfara ta gyara wadannan bangarorin insha Allah mutane za su samu sauyi mai ma’ana.

Allah Ya ci gaba da wanzar da tsaro da kuma arziki mai albarka a cikin Jihar Zamfara da Najeriya baki daya.

Yakubu Usman, [email protected]  08166756463