Da Dumi Dumi
ADVERTISEMENT

Shawara ga ma’aurata (1)

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu.

Na yi wannan rubutu wanda yake shawarwari ne ga masu niyyar yin aure kuma na tsakuro kadan daga cikin shahararren littafin nan ne nawa mai suna “Manyan Dalilai 50 Da Ke Kawo Mutuwar aure”.

ADVERTISEMENT

Da fatar za mu amfana kuma mu isar ga wadanda ba su same shi ba.

 

ADVERTISEMENT

Kamar yadda muka sani aure ibada ne kuma Sunnah ce ta kowane Manzo da Allah Ya aiko.

 

1- Yadda ake neman aure a Musulunci

A bisa tanadi na shari’a duk abin da kake nema dole ka nemi izinin mai mallakarsa, don haka wajibi ne ga wanda ya ga yarinya yana sonta da aure ya nemi izinin magabatanta, su kuma in sun ba wani izini ba ya halatta su sake ba wa wani dama har sai wancan ya janye kamar yadda ya zo a fadar Annabi Muhammad (SAW) inda yake cewa “Kada waninku ya nemi aure a cikin neman wani har sai wancan ya janye ko kuma an yi masa izini.”

2-Namijin da ya kamata mace ta aura

Annabi (SAW) ya ce “Idan wanda kuka yarda da addininsa da dabi’unsa ya zo neman auren ’yarku, ku aurar masa idan ba haka ba fitina za ta yadu a bayam kasa da barna mai girma.”

Abubuwa uku ake nema ga namijin da za a ba aure:

1- Mai addini

2- Mai kyakyawar dabi’a

3- Mai aikin yi

3- Macen da namiji ya kamata ya aura

A nan idan muka duba kowane da irin sha’awarsa ga macen da yake so. Lura da haka Annabi (SAW) ya ce “Ana auren mace don abubuwa uku:

1- Saboda dukiyarta

2- Saboda kyawunta

3- Saboda nasabarta

4- Saboda addininta.

Sai ya ce “Amma ina umartar ku da ku auri ma’abociyar addini,sai hannuwanku su rabauta.”

4- Hakkokin mace a kan mijinta

1- Samar da muhalli

2- Ciyarwa da shayarwa

3- Tufatarwa

4- Kula da addininta

5- Biyan bukatar sha’awarta

6- Kula da lafiyarta

7- Tsare mutuncinta

8- Tsare dukan bukatunta na wajibi.

5- Hakkokin miji a kan matarsa

1- Yi masa biyayya a bisa shari’a

2- Tsare mutuncin kanta

3- Kula da dukiyarsa

4- Kula da tarbiyyar ’ya’yansa

5- Tsare sirrinsa.

Za mu ci gaba insha Allah.

Sanusi Hashim Abban Sultana daga Jihar Katsina

08065507271

abbansultana2018@gmail.com