Categories: Daga Masarauta

Shawara ga ma’aurata (2)

Assalamu alaikum masoya wannan fili mai fadakarwa a kan abin da ya shafi iyali yau ma ga ni da karashen rubutun da na fara kimanin mako biyu da suka wuce kamar yadda na yi alkawari.

6- Daren Tarewa:

ADVERTISEMENT

Akwai ladubba da ma’aurata ya kamata su lazumta (aikata) a darensu na farko wato ranar tarewa;

1- Ango zai shiga da sallama tare da addu’ar shiga gida

ADVERTISEMENT

2- Ango zai shiga da kayan makulashe kamar naman kaza da madara ko nono da kayan itatuwa daidai gwargwadon ikonsa

3- Amarya za ta caba ado tare da feshe jikinta da kayan kamshi don tarbar angonta

4- Za su yi alwala sannan su yi Sallah raka’a biyu sai ya cire kallabinta ya dafa goshinta ya karanta “Allahumma inni as’aluka min khairiha wa khairi ma jabaltaha alaihi, wa a’uzubika min sharriha wa sharri ma jabaltaha alaihi”.

5- Sai ango ya yi mata nasiha su yi musayar tausasan kalamai na kauna da jaddada rikon amana da kula da tausayin juna da kiyaye hakkokin juna.

6- Addu’ar saduwa:

Annabi (SAW) ya ce “duk wanda ya karanta wannan addu’ar yayin saduwa da iyalinsa Allah Zai tsare abin da aka samu daga Shaidan” ga ta kamar haka: “Allahumma jannibni-shaidana wa jannibib-shaidana ma razakatana”.

7- Tsarki:

Tsarki ya kasu gida uku;

1- Tsarkin zuciya: Mutum ya bauta wa Allah Shi kadai kada ya hada Shi da wani wajen bauta kuma wanin ko wane ne, sannan ya yi koyi da Annabi (SAW) in zai yi ibadar.

2- Tsarkin jiki: Shi ma ya kasu gida biyu, tsarki na jiki wanda mutum zai yi wanka ya caba ado sai tsarki na kari wato mutum ya yi wankan tsarki wanda zan kawo shi nan gaba.

3- Tsarki na wuri: Yadda mace za ta kula da tsabtace muhallinta.

Abin da ya shafi shara, goge dakuna da ruwa, wanke kewaye (bayi) da sauransu.

Akwai matar da in ka leka karkashin gadonta ko kujerunta za ka ga tulin kayan wanki.

Wajibi ne mace duk rana ta share gidanta akalla sau biyu sannan ta goge, kuma bayan lokaci zuwa lokaci ta rika daga gadonta da kujerunta tana sharewa gami da canja musu waje ta yadda in maigida ya shigo zai ga kamar sabuwar amarya aka kawo masa.

8- Yadda ake yin wanka:

Akwai nau’o’in wanka kamar haka:

1-Wankan shiga Musulunci

2-Wankan Janaba

3-Wankan Haila

4-Wankan Jinin Biki

Wadannan su ne wanka na wajibi kuma dukansu yadda ake yin su daya ne sai dai bambancin niyya.

Mu kwana nan

Sanusi Hashim Abban Sultana

Daga Jihar Katsina

08065507271

abbansultana2018@gmail.com

. .

Recent Posts

Kasafin Kudi: Za a kashe wa tsofaffin shugabannin Najeriya Naira Biliyan 2.3

Gwamnatin tarayya zata kashe wa tsofaffin shugabannin Najeriya da mataimakansu, dama manyan hafsoshin mulkin soja, kudade sama da Naira biliyan…

2 hours ago

Amsoshin tambayoyin daban-daban: Ranar Allurar Barci ta Duniya

A da idan aka ji an ce za a yi wa mutum tiyata, ba abin da ke zuwa ran wanda…

3 hours ago

Amsoshin Tambayoyi

Mace mai ciwon sanyi idan ta samu juna biyu wane irin magani ya kamata ta yi amfani da shi ko…

3 hours ago

Maraba da dokar hana sakin aure a Jihar Kano (6)

A yau cikin ikon Allah za mu karkare wannan batu da muka faro kimanin makonni 5 da suka gabata. Idan aka…

3 hours ago

An kama ango da amarya kan ba da mafaka ga masu garkuwa da mutane

Al’ummar Unguwar Jiwafa da ke Sabon Garin Marabar Gurku a Jihar Nassarawa na ci gaba da zaman dar-dar, mako biyu…

3 hours ago

Mun yaba da rufe kan iyakoki Najeriya

Hakika rufe kan iyakoki da gwamnatin Shugaba Buhari ta yi domin inganta tattalin arzikin kasar abin yabawa ne sosai. Duk…

3 hours ago