Search
Subscribe
Shawara ga matasa game da rayuwa

Shawara ga matasa game da rayuwa

Kamar yadda kanun maudu’inmu na yau ya nuna, za mu ba da wasu shawarwari ne na musamman ga matasanmu game da al’amuran rayuwa. Kodayake mun taba ba matasan shawara a daya daga cikin bayananmu, sai dai a wannan karo, na samu bukatar haka ne daga wani ma’abucin karanta wannan fili, Malam Hashim Kafinta, Layin NYSC, Kongolam, Jihar Katsina, wanda ya aiko da sakon tes kamar haka:

Assalamu alaikum. Don Allah ina fatan wata rana wannan fili namu zai yi sharhi game da mutane masu ji-ji-da-kai, musamman matasa. Misali, za ka ga wani matashin saboda ya tashi a gidansu akwai kudi ko mulki, bai damu da girmama na gaba da shi ba; ko duk wata harka da za ku yi da shi sai ya wulakanta ka, saboda shi a tunaninsa, ya fito daga gidan manya. Ko kuma budurwar da za ta dauki karya ta dora wa kanta, alhali wata ma mahaifinta ba kowa ba ne.”

To, Malam Hashim, ga shi yanzu mun amsa kiranka, kuma za mu dan yi tsokaci game da wadannan bayanai naka, tare da fatan za mu amfana da dan abin da hankalinmu zai tsokanta. Babbar fa’idar dai ita ce, mu samu tsira daga wannan mawuyaciyar rayuwa ta duniya.

Bari mu dauki al’amari na farko da ka kawo, wato batun irin matasan nan masu takama da dukiyar iyayensu ko ganin cewa iyayen nasu na da mulki, wanda ka ce wannan ke sanyawa su dora wa kawunansu girman kai; kuma hakan ke sanyawa su rika wulakantawa da raina mutane. A nan, ya kamata irin wadannan matasa su gane cewa, al’amarin rayuwa ya zarce iya tunaninsu, domin kuwa mafi yawan lokaci, ita duniya wata mushkila ce mai rudin rudaddu, mai karkatar da masu karancin tunani, mai jefar da duk wanda ya rungume ta kuma ya ba ta gaskiya.

A nan, ya kamata matasa masu takama da daukakar iyayensu su fahimci cewa, duk mukamin da iyayen nasu suka samu, walau dukiya ko mulki, ba su same su ne a rana tsaka ba, kuma babu wai ba inke, ba gado suka yi ba. Idan ma gadon ne suka yi, to lallai sun ladabtu, sun wahaltu kafin su samu damar rike wannan dukiya ko mulki. Ke nan su sun ga nasu, to kai kuma fa matashi? Maimakon ka dauki girman kai ka dora wa kanka, kamata ya yi ka kwantar da kanka, ka binciki tarihi, ta yaya iyayen naka suka samu wannan daukaka? Wace hanya suka bi har suka zama abin da suka zama? Babu shakka ina da yakinin cewa duk wanda ya zama karkatacce a lokacin kuruciyarsa, ba zai samu nasarar daukaka ba. Don haka, ina da yakinin cewa iyayen nan naku da suka samu daukaka, sun sha wahala lokacin kuruciyarsu, sun tashi tsaye sun nemi hanyar daukaka a rayuwa, ba su wulakanta mutane ba, kuma ba su sanya girman kai a zukatansu ba.

Abu ne sananne cewa, shi girman kai rawanin tsiya ne, don haka duk matashin da ya sanya wa kansa girman kai, to ga shi can hanyar lalacewa da balbalcewa a rayuwa. Tarihi yana maimaita kansa ne a dukkan lokaci, domin ban taba ji ko ganin wani mai girman kai ya samu fa’idar rayuwa ba. Idan haka ne, ya kamata matasa su jefar da wannan mummunan hali na girman kai, su rungumi kyawawan dabi’u domin samun fa’idar rayuwa.

Game da rashin ladabi da wulakanta jama’a kuwa, su ma wadannan wasu munanan halaye ne masu dakile azamar duk mai yinsu. Babu shakka inda akuyar gaba ta sha ruwa, nan ta baya za ta sha. Don haka, wadannan munanan halaye, duk uwarsu daya ubansu daya da girman kai. Babu wanda zai samu a yi masa ladabi idan shi bai yi wa wani ba; haka duk wanda ya kasance mai wulakanta jama’a, to shi ma ba zai kai labari ba, domin kuwa shi ma ga shi can a wulakance, yau ko gobe. Wannan kuwa gaskiya ne, domin mutane na da wata daraja ta musamman, kowa akwai albarkar da Allah Ya zuba masa, koda kuwa bai mallaki dukiya ko mulki ba. Don haka duk wanda ya ce zai wulakanta jama’a, to ba zai sha da lafiya ba. Ya kamata matasa masu irin wadannan halaye su yi saurin dainawa, kuma su rika mutunta mutane, suna ba kowa hakkinsa daidai gwargwado. Ta haka ne mutum zai wanye da jama’a lafiya, sannan kuma ya wanye da duniya salamun-salamun.

Sai kuma mu koma kan batun Malam Hashim, inda ya yi batun misalin budurwa mai karya da ji-ji-da-kai duk kuwa da cewa ita ba ’yar kowa ba ce. To, duk dai sawa’un da batun matasan farko, domin duk bikin Magaji ne, bai hana na Magajiya. Kamar yakin ruwa ne da ya ci sakaina, ta ce mu je zuwa. Babu abin da za mu ce da irin wadannan mata sai dai mu ce kamar sun makara a rayuwa, muddin suka ce za su dauki wannan turba ta karya da son a sani, alhali ba haka al’amarin yake ba. Shi dai ramin karya kurarre ne, duk wanda ya ce zai shiga cikinsa, to ba zai rufa masa asiri ba, domin ba da jimawa ba asiri zai tonu, gaskiya za ta yi halinta. A yadda duniya ta sukurkuce, babbar hanya, mikakkiya ita ce abar bi, wacce za ta kai mutum ga mafita, amma ba karya ba da gadara.

Ba zan mace da maudu’in da muka tattauna a kansa ba a kwanakin baya, domin kuwa akwai wani sashi da ya kamata in tsamo daga ciki domin ya sake fa’idantar da matasanmu a nan. Mun yi bayani ne game da masu shashantar da kansu, su watsar da al’amuran rayuwa, har ma su shantake cewa ba za su samu nasarar rayuwa ba. A cikin bayanin namu, akwai inda muka ce:

“Ita nasara fa babu ruwanta da gado, babu ruwanta da cewa babana kaza ne, innata kaza ce, yayana kaza ne. Kowa na iya samun nasara, muddin ya bi matakan da suka dace. Kana gani, dan talaka sai ya zama shugaba, idan dai ya bi matakan zama shugaban. Kana gani dan attajiri zai tsiyace, idan bai bi matakan zama attajirin ba. Haka kuma dan malami na iya zama kuntukurmin jahili, muddin bai bi matakan da zai samu ilimi ba. Don haka, rayuwa ’yar tashi a nema ce, kuma neman za a yi shi ne ba da sanyin jiki ba. Za a jajirce, sannan a maida hankali, idan da rabo sai nasara ta kawo jiki da kanta.”

Shin ko matasanmu za su fahimci wani abu daga wannan bayanin na sama? Ko za su yi wa kawunansu matashiya, sannan su yi wa kawunan nasu fada domin su canja alkiblar rayuwa? Domin kuwa al’amarin rayuwa kamar yadda muka ambata can a baya, wani abu ne mai wahalar ganewa, kuma mai wahalar sha’ani. Amma duk iya wahalarsa da muskilancinsa, matukar mutum ya bi shi da taka-tsantsan, lallai zai samu nasarar wanyewa da rayuwa lafiya, har ma a ce masa sam-barka. Ke nan ya dace mu tunkari duk abin da ya kamata na rayuwa cikin fa’ida da tawali’u da sanin ya kamata.

Shawara ta musamman ga matasanmu maza da mata ita ce, lallai su yi wa kansu kiyamul laili, su fuskanci lamarin gaskiya, su watsar da karya da bagu da rayuwar bogi. Su mutunta kawunansu sannan su mutunta abokan zamansu, su fitar da girman kai da gadara. Idan suka yi haka, nasarar rayuwa za ta kasance tasu, ko yau ko gobe. Allah Ya sanya mu dace, amin.

  • facebook
  • twitter
  • whatsapp
  • linkedin