✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shayar da jarirai: Hannunka-mai-sanda ga mata (3)

Kasancewar nonon uwa tatacce ne kuma tsabtataccen abinci da Allah (SWT) Ya tanada don jarirai, ya kunshi duk sinadaran abinci wadanda jarirai ke bukata wajen…

Kasancewar nonon uwa tatacce ne kuma tsabtataccen abinci da Allah (SWT) Ya tanada don jarirai, ya kunshi duk sinadaran abinci wadanda jarirai ke bukata wajen gina jiki da samar da kuzari da kuma ba da kariya daga kwayoyin cuta.

Bincike ya tabbatar da cewa shayar da nonon uwa na iya rage hadarin kamuwa da ciwon yunwa, wato tamowa da sauran cututtuka masu alaka da karanci da ingantaccen abinci.

Kuma ya kamata mu sani cewa, duk wani nau’in abinci da ake amfani da shi a madadin nonon  uwa ba zai taba samun  inganci, kamar na nonon uwa ba, duk adadin kudin da za a kashe wajen hada shi. Ko ba komai, akwai hadarin shigar kwayoyin cuta  yayin hada abincin ko wajen ajiya da kuma wajen bayarwa.

Shayar da nonon uwa zalla na tsawon wata shida na taimaka wa uwa wajen komawar mahaifa da wuri bayan haihuwa, wanda hakan zai taimaki jikinta ya murmure tare da rage yiwuwar sake daukar wani cikin da wuri.

Shayar da nonon uwa na kara (sanya) shakuwa da kauna a tsakanin uwa da jaririnta. Kasancewar nonon uwa abu ne daga Allah, wanda ba sayensa ake yi ba, shi kansa mai gida zai samu saukin dawainiya, ta yadda zai iya amfani da rarar kudinsa don yin wata hidima ta iyali, maimakon sayo madarar da za a hada wa jariri.

Tunanin da wadansu ke yi cewa idan ba a bai wa jariri ruwa zai galabaita sam ba gaskiya ba ce. Domin binciken masana ya tabbatar da cewa kashi 88 cikin 100 na sinadaran da nonon uwa ya kunsa ruwa ne. Don haka jarirai ba sa bukatar karin wani ruwa, bayan wanda suke samu daga cikin nono. Iyaye da dama wadanda suka gwada shayar da nonon uwa zalla na wata shida, sun tabbatar da ingancin hakan wajen kara lafiyar jarirai da kuma tasirin da hakan wajen girman jikinsu da kuma kaifin kwakwalwarsu bayan sun girma.

Domin karfafa wannan tsarin na shayar da nonon uwa zalla na tsawon wata shida, akwai bukatar shugabannin al’umma a matakai daban-daban su kara fuskantar wannan tsari tare da ba da gudunmawa,  wajen wayar da kan al’umarsu, domin aiwatar da shi yadda ya kamata.

Su ma iyaye maza magidanta na da muhimmiyar rawar takawa wajen taimaka wa mata masu raino ta wajen kula da bukatansu na abinci da na lafiyar jariran da suka haifa musu. Akwai kuma bukatar wadata su da ingantattun abinci da kayan marmari don taimaka wa murmurewar jikinsu da kara yawa da ingancin nonon da suke shayar da jariransu.

A hukumance kuma, akwai bukatar samar da dokokin da za su karfafa gwiwar iyaye mata su aiwatar da tsarin shayar da nonon uwa zalla na wata shida. Misali, ga mata masu aiki a hukomomin gwamnati da masu zaman kansu, akwai bukatar a duba yiwuwar kara tsawon hutun haihuwa daga wata hudu zuwa wata shida; tare da samar da dakin raino a kowace mai’aikata don bai wa mata ma’ikata damar shayar da jariransu nono yadda ya kamata.