Da Dumi Dumi

Shayar da jarirai: Hannunka-mai-sanda ga mata

A kwanakin baya ne aka gudanar da bikin makon shayar da jarirai nonon uwa na duniya. Bikin dai wata dama ce da kwararru a harkar lafiyar kananan yara na kowace kasa ke amfani da shi domin jadadda muhimmancin shayar da jarirai nonon uwa tare da warware wasu mas’aloli da suka danganci haka. Taken bikin shi ne: “Waiwayen baya, don fuskantar gaba.”

A Najeriya, shayar da jariri nonon uwa ya kasance abu mai asali, wanda kusan za a iya cewa babu wata kabila da ba ta shayar da jariranta nonon uwa. Wani bincike na Hukumar NDHS (2008), wanda aka gudanar a karkashin Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) ya nuna cewa, mafi yawan kananan yara a Najeriya na samun shayar da nonon uwa har na tsawon wata goma sha takwas kafin a yaye su.

Sai dai alkaluman binciken sun kuma nuna cewa, kashi goma sha uku ne cikin dari kacal ne na jariran ke samun shayar da nonon uwa zalla na tsawon wata shida, kamar yadda hukumomin lafiya suka bukaci a yi.

Don haka a inda gizo yake sakar shi ne, lokacin da ake fara shayarwar, da kuma yanayin yadda  ake gudanar da ita.

Mu kwana nan

ADVERTISEMENT

 

Share
A latsa wannan alamar domin shiga zauren Jaridar Aminiya