✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shaye-shayen miyagun kwayoyi a tsakanin matasa: Ina mafita? (2)

A makon jiya ne muka gabatar da kashi na farko na jawabin ALHAJI IBRAHIM AHMAD KATSINA,Shugaban Gidauniyar Samar da Dauwamammen Zaman Lafiya ta Fannin Tsaro…

A makon jiya ne muka gabatar da kashi na farko na jawabin ALHAJI IBRAHIM AHMAD KATSINA,Shugaban Gidauniyar Samar da Dauwamammen Zaman Lafiya ta Fannin Tsaro da Zamantakewar Al’umma), lokacin da ya kasance babban bako mai jawabi a taron Kungiyar Gizago ta Kasa da aka gudanar a Katsina ranar Asabar22-09-2018), takardar tana magana ce kan illolin tu’ammali da miyagun kwayoyi; ga ci gaba:

Wane ne mashayin kwaya?

Za a iya kiran mutum da mashayin kwaya, a lokacin da ya ta’allaka rayuwarsa kacokan ga amfani da kwayoyin da aka haramta ko kuma wadanda yake sha ba tare da umarnin likita ba (Ibrahim, 2016).

Abubuwan da suke haddasa tu’ammali da kwaya:

Abubuwan da suke haddasa tu’ammali da kwaya suna da yawa, musamman ga matasa. Wadannan abubuwa sun hada da kuruciya da jaraba shan kwaya don jin yadda take, domin samun annashuwa da maganin damuwa ko kuma zama da mashaya. Kamar yadda binciken wani masani mai suna Odejide (2014) ya nuna.Wasu daga cikin dalilan da matasa masu shaye-shaye suka bayyana dangane da kwaya su ne: Domin mu ji cewa mu isassu ne kamar manya ko domin mu kasance cikin nishadi ko domin mu kasance kamar abokanmu ko don mu ji mu cikin wattsakewa ko don mu rika jin kamar mu taurari ne. Babu shakka, shaye-shayen miyagun kwayoyi kan haddasa matsaloli ga su kansu matasan da kuma al’umma. Wasu daga cikin abubuwan da ke taimakawa wajen yaduwar tu’ammali da miyagun kwayoyi sun hada da:

’Yan siyasa:

Wadansu gurbatattun ’yan siyasa kan yi amfani da matasan da suka siffatu da tu’ammali da kwayoyi wajen cimma wasu munanan bukatunsu. Haka kuma, wannan muguwar ta’ada ce ke haifar da daba a tsakanin matasa. Matukar ba a bincika an magance ta ba, matasanmu za su rasa tagomashi, za su lalace gaba daya a rayuwarsu, wanda haka zai  kara zama barazana ga al’umma, ya haifar da rashin tsaro da lalacewar kasa gaba daya.

Lalaci da zaman kashe wando a tsakanin matasa:

Zaman kashe wando, wato rashin aikin yi ko sana’a da lalaci a tsakanin matasa na daga cikin abubuwan da kan ingiza matasan ga tu’ammali da miyagun kwayoyi, kuma daga bisani hakan kan haifar da aikata miyagun laifuffuka. Wani abu da yake karara a cikin al’ummarmu shi ne, matasanmu malalata ne, wadanda suke son jin dadin rayuwa a saukake, ba tare da sun yi aiki ko sana’a ba. Wannan dalili ne ke sanya su raina duk wata karamar sana’a ko karamin aiki da zai shagaltar da su. Lallai ya kamata a samo hanyoyin magance wannan hali daga matasanmu, idan ba haka ba kuwa, al’amarin zai ta’azzara.

Yawaitar tu’amali da miyagun kwayoyi a cikin al’umma:

Irin yadda tu’ammali da miyagun kwayoyi ke bunkasa a cikin al’umma kamar wutar daji, abin ta da hankali ne. Idan aka lura, mafi yawan shagunan sayar da magani, an mayar da su bigiren sayar da miyagun kwayoyi. Wannan muguwar sana’a, ita ce ke cin kare ba babbaka a lunguna da sakon gaururuwanmu da karkara.

Hauhawar manyan laifuffuka a kasa:

A wannan zamani, manyan laifuffuka na kara hauhawa, musamman saboda saukin hanyoyin sadarwa a sanadiyyar fasahar sadarwa da ta saukaka. Mu duba dai yadda ta’addancin kwacen dukiyar al’umma ya ta’azzara ta hanyar amfani da tsinin bindiga, yadda ake kama mutane domin amsar kudin fansa, yadda kuma fashi da makami yake karuwa kuma abin takaici, matasa ne kan gaba cikin wannan aika-aika.

Yadda matasa suka rasa sahihan jagorori:

A yau, matasanmu sun rasa sahihan jagorori abin koyi a cikin al’umma kuma wannan na daya daga cikin dalilan da suka sanya matasan namu suka shiga lalacewa da shaye-shaye da aikata miyagun laifuffuka. Shugabannin al’umma sun banzatar da matasa, ba su jawo su a jika suna koya masu tarbiyya da ba su jagoranci na kwarai. Dalili ke nan matashi kan rasa tudun dafawa, yake jin cewa an watsar da shi, wanda kuma hakan ke ingiza shi ga shaye-shaye da aikata miyagun laifuffuka.

Wata kungiya a Amurka da ke bibiyar al’amuran da suka shafi tabin hankali ta yi wani bincike a shekarar 2000, inda ta gano cewa akwai wasu abubuwa uku da ke ingiza matasa zuwa ga shaye-shayen miyagun kwayoyi, kamar haka:

1-Yanayin halayya: Canjin halayyar matasa da ta shafi jin dadinsu ko rashin natsuwa ko damuwa ko zumudi kan iya taka rawa wajen saka su ga shaye-shaye.

2-Abokan zama: Yanayin abokai kan sanya matasa su canja halayyarsu. Idan matasa suka kasance masu shaye-shaye a unguwa, hakan kan zama abin koyi ga sauran matasa. Haka kuma matasan da suka fito daga gidajen talauci ma kan yi saurin fadawa cikin harkokin shaye-shaye. Su kuwa Abuh da Akus (2009), sun bayyana cewa abubuwa biyu ne ke ingiza matasa zuwa ga shaye-shaye, wato tarayya da miyagun abokai da kuma yanayin damuwa.

3-Tarayya da miyagun abokai: A lokacin da matashi ya tsinci kansa cikin gungun miyagun abokai, abu ne mai yiwuwa ya biye musu, ya dandana shan kwaya ko sau daya, daga nan kuma zai ci gaba har ta zame masa jiki.

4-Yanayin damuwa: Idan matashi ya shiga wani yanayi na damuwa, kamar rashin abin yi ko faduwa jarabawa ko kuma idan wani abin takaici ya faru gare shi, akwai yiwuwar ya fara tunanin fara shan kwaya ko giya da nufin magance wannan yanayi da ya samu kansa a ciki, wanda daga bisani sai abin ya zama halayyarsa, kwaya ta kama masa jiki ya zama mashayi.

Wasu daga cikin dalilan kuma, kamar yadda Ballas (2006) ya gano, sun hada da dabi’ar kuru da matasa kan nuna da bijire wa al’ada da tsunduma cikin shaye-shaye tun suna kanana da rashin samun tarbiyya daga iyaye da rashin daraja kai da rashin fikirar magance halin damuwa da kokarin kauce wa yanayi na hakika da kuma neman jin dadin rayuwa ta hanya mai sauki.