✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Shehun Borno ya bukaci a kara kaimi wajen yaki da ta’addanci

Mai martaba Shehun Borno Alhaji Abubakar Umar Garbai Al-Amin EL-Kanemi, ya bukaci Gwamnan Jihar Borno ya ci gaba da mayar da hankali a kan inganta…

Mai martaba Shehun Borno Alhaji Abubakar Umar Garbai Al-Amin EL-Kanemi, ya bukaci Gwamnan Jihar Borno ya ci gaba da mayar da hankali a kan inganta tsaro don samun kwanciyar hankali da zama lafiya a jihar.

Shehun ya yi wannan kira ne lokacin da ya kai zaiyarar Gaisuwar Sallah ga Gwamnan Jihar Farfesa Babagana Umara a Gidan Gwamnati da ke Maiduguri.

Ya kara da cewa, “Babu shakka idan Gwamnatin Tarayya da na jiha suka mayar da hankalinsu wajen inganta harkar tsaro da dakile ayyukan ’yan ta’adda, to al’ummar jihar za su samu cikakken kwanciyar hankali da zaman lafiya da ingantuwar tattalin arziki, ta yadda kowane dan gudun hijira da yake Maiduguri da sauran wuraren zai iya komawa garinsu babu fargaba, kuma su iya gudanar da noma da kiwo da  kasuwanci a tsaninsu da makwabtansu. “Duk da cewa gwamnati da jami’an tsaro suna kokari wajen tabbatar da dawowar zaman lafiya a jihar, amma akwai bukatar a kara kaimi wajen dakile kananan hare-haren da ’yan bindiga ke kaiwa nan da can, don a ce suna nan alhali karfinsu ya kare, kawai suna tsorata mutane ne tare da karya musu karfin gwiwar komawa garuruwansu,” inji shi.

Shehun ya bukaci Gwamnan ya mika wannan kuka nasa zuwa ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari don daukar mataki na gaba.

Da ya juya kan tarbiyyar yara kuma, Shehun ya nuna bakin cikinsa game da komowar harkokin batagari a wasu wurare da gwamnati ta haramta musu, don haka ya bukaci Gwamnan ya duba  wannan al’amarin don gyarawa.

Da yake mayar da jawabi, Gwamna Babagana Umara ya ce, “Babu shakka yana daya daga cikin kudirin gwamnatina bunkasawa tare da samar da ingantaccen tsaro da zama lafiya a wannan jiha da ta sha fama da ta’addanci na tsawon shekaru da ya yi sanadiyyar rasa rayukan dimbin jama’a tare da raba wasu da muhallansu. Babu shakka gwamnatina da hadin gwiwar jami’an tsaro na tarayya muna kokarinmu wajen dawo da ingantaccen tsaro da zaman lafiya ta yadda al’umman jihar za su ci gaba da gudanar da harkokin rayuwarsu na yau da kullum babu wani tsangwama. Don haka muna nan muna iya kokarinmu, abin da muke bukata kawai a wajen al’umma shi ne addu’o’i gami da hakuri.”