Sheikh Dahiru Bauchi yana nan lafiya kalau

Sheikh Dahiru Bauchi
Sheikh Dahiru Bauchi
Iyalan sananen malamin addinin musulunci Sheikh Dahiru Usma  Bauchi sun karyata jitajitar da ake yadawa cewa ba shi da lafiya yana kwance, inda suka ce shehin yana nan lafiya kalau.
Daya daga cikin Hadimansa Alhaji Sanusi Ahmad Dahiru  ya ce shehin yanan lafiya, kuma yanzu haka ma ya tafi aikin umarah ranar Juma’ar da ta gabata kuma yana cikin koshin lafiya.
Sanusi ya ce a a kwanakin baya ma wadansu mutane sun ta yada jita-jitan  cewa ya rasu.
Sai ya roki Allah Ya ja kwanan shehi Ya kara masa lafiya.
Wannan karin hasken yana zuwa ne bayan wasu kafafen watsa labarai sun ta yada jita-jitar cewa shehin yana kwance ba shi da lafiya.

Share