Aminiya

Sheikh Jingir ya shawarci Shugaba Buhari ya dauki mataki kan ’yan Shi’a

Sheikh Sani Yahaya Jingir

Shugaban Majalisar Malamai ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’a Wa Ikamatis Sunnah ta Kasa, (JIBWIS) Sheikh Sani Yahaya Jingir, ya shawarci Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dau matakin da ya dace a kan tayar da rikici da kai hari ga jami’an tsaro da sauran ’yan Najeriya da Kungiyar IMN  ta ’yan Shi’a mabiya Zakzaky suke yi, domin hana faruwar haka a nan gaba.

A jiya Alhamis ce Sheikh Sani Yahaya Jingir ya  bayyana haka a wata tattataunawa da ya yi da manema labarai a ofishinsa da ke garin Jos.

ADVERTISEMENT

Ya ce a matsayin Kungiyar Izala ta ta kungiyar addini ba za ta zuba ido ta kyale rikicin ya zama ya girmama ba.

Ya ce, “Abin takaici ne a ce ’yan kasa su dauki makamai a hannunsu su kai farmaki ga jami’an tsaro, sannan su yi yunkurin kai hari ga Majalisar Dokoki sannan su rika ikirarin za su kashe ’ya ’yan Shugaban Kasa ko kuma Shugaban Kasa. Muna so Shugaban Kasa kada ya dauki wannan batun da wasa, lallai ya dauki matakin da ya dace a kai. Kuma jami’an tsaro su tabbatar sun dauki matakin da ya dace domin dakile irin wannan hali na ’yan Shi’a.”

ADVERTISEMENT

Sannan ya shawarci sanatoci da kada su tantance duk wani ministan da yake da alaka da wannan kungiya ta Shi’a domin suna ikirarin wargajewar Najeriya.